✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rikicin Falasdinawa da Isra’ila ya tada hankulan shugabannin duniya

Tuni dai manyan shugabannin duniya suka fara tofa albakacin bakinsu kan rikicin.

Shugabanni a sassan duniya na ci gaba da yin tsokaci kan yadda rikicin Falasdinawa da Isra’ila ke kara da tsananta ba tare da alamun kawo karshensa a nan kusa ba.

A ganawarsa ta waya da Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, Shugaban Amurka, Joe Biden, ya bayyana kaduwarsa, tare da nema wa ’yan jarida kariya, sannan ya bukaci a shirya taron gaggawa don nemo mafita.

Ofishin Jakadancin Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci Biden da shugaban Hukumar Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar, Michelle Bachelet, da su nemo mafita kan rikicin da ke salwantar rayukan daruruwan mutane.

Kazalika, Kamfanin Dillacin Labarai na AP, gidan talabijin na AlJazeera da wasu kafofin watsa labarai sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda Isra’ila ta rushe ginin da suke ciki da gangan.

A nasa bangaren kuwa, kakakin shugaban kasar Turkiyya, Fahrettin Altun, ya yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai wa kafafen watsa labarai.

Ita ma, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da su gaggauta kawo karshen hare-haren da Isra’ila da Falasdinawa ke kaiwa juna, tare da yin Allah wadai da hakan.

Tuni dai dubban mutane daga sassan duniya, ta kafafen sada zumunta, suka shiga bayyana ra’ayoyinsu tare da alhini game da yadda rikicin ke salwantar da rayukan wanda ba su ji ba, ba su gani ba.