✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ronaldo ya shafe awa 7 a layin shan mai a Burtaniya

Rahotanni sun ce ta sa ya hakura bayan shafe awa bakwai a kan layi.

Motar fitaccen dan wasan kwallon kafar nan, Cristiano Ronaldo wacce ta kai £220,000 ta shafe awa bakwai a wani gidan mai a kasar Burtaniya ba tare da ta samu sha ba.

An dai hangi motar dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a layin shan mai a Wilmslow, amma tilas ta sa ya hakura ba tare da ya samu ba.

Matsalar wahalar mai dai ta kunno kai ne a kasar ta Burtaniya, kuma da alama tana ci wa masu karamin karfi da ma masu hannu da shuni tuwo a kwarya.

Hukumomin kasar dai sun ce ana samun saukin matsalar sabanin a karshen makon da ya gabata.

Sai dai Sakataren Kudin kasar, Simon Clarke ya tsaya kai da fata cewa lamarin zai zama tarihi nan ba da jimawa ba matukar mutane suka koma rayuwarsu kamar yadda suka saba.

Rahotanni dai sun ce motar dan wasan kirar Bentley ta shiga gidan mai ne tun wajen misalin karfe 2:20 na rana, amma har zuwa misalin karfe 9:00 na dare yana kan layi, daga karshe da direbansa ya tabbatar ba za su samu ba sai ya hakura ya fita haka.

Wani ganau a inda lamarin ya faru ya ce, “Duk kudin da Ronaldo yake da shi, haka ya tsaya a kan layi kamar sauran mutane ya-ku-bayi.”

To sai dai rahotanni sun ce hakan bai bata masa rai sosai ba, saboda ko a safiyar ranar Juma’a an hange shi a daya daga cikin motocinsa na alfarma kirar Porsche zai tafin wajen bayar da horo.