✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sana’ar suya da sayar fara ke taimaka wa mata a Maiduguri

Na kan yi cinikin Naira 3,000 a kullum.

A Maiduguri babban birnin Jihar Borno, ba bakon abu ba ne ka ga mata na sayar da soyayyar fara a bakin titi.

Za ka ga wadannan mata ne a tasoshin mota da kasuwanni da kuma wasu wurare a manyan titunan birnin, inda kuma mutane ke cincirindo domin saya.

Da sanyin safiya, misalin karfe 6:00 za ka ga irin wadannan mata daga unguwanni daban-daban da ke ciki da kuma wajen garin Maiduguri sun soma tururuwa zuwa kusuwar da ake kawo farar daga daji domin sayen farar sabon kamu ko kuma tsohon kamu wacce aka ajiye, aka kuma alkinta.

Wadannan daruruwan mata masu sayen farar don suya, su ke samar wa da dimbin matasan da ke fita farautar wannan kwaron a dazukan da ke kasashen Chadi da kuma jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da Kasar ta jihar Borno aikin yi, inda su kuma ke sayar wa musu saye ba kakkautawa don su mayar da kwalamarsu.

Mary Adamu, wata matar aure da ’ya’ya biyar na daga cikin wadanda suke sana’ar suyar fara da sayar da ita ga jama’a, inda ta kwashe shekara takwas tana yi, kuma da ita take kula da karatun ‘ya’yanta.

“Na kan yi cinikin Naira 3,000 a kullum, wani lokacin cinikin yakan fi haka.

“Da kuma kudin ne nake biyan kudin makarantan yarana da kuma sauran bukatu na yau da kullum, har ma na taimka wa dangina daga cinikin,” inji Mary.

Mary wacce dimbin masu sayen farar ke kewaye ta a wurin da take sanarta, inda a wannan lokaci na hada-hadar sayen farar muka yi hira da ita, ta ce, “ban san iya adadin matan da ke wannan sana’a ba a garin nan, saboda idan ka kewaya titunan Maiduguri, za ka ga inda mata ke suyar farar sun fi dubu, domin sana’a ce da mata suka fi yawa a ciki, amma wajen suya kawai da sayarwa.

“Amma maza su ne ke zuwa daji su kamo farar.

“Daga dukkan alamu kasuwar soyayyiyar farar ta bunkasa, kasancewar safarar farar da ake yi daga cikin Maiduguri zuwa wasu wajen jihar, a cewar Mary, ita kanta tana da kwastomomi a wasu jihohi ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja.

“Mutane na zuwa su saya da yawa domin aika wa ‘yan uwa da abokai da kuma dangi da ke garuruwa irin su Kano da Katsina da Jos har da Abuja.”

Mary ta ce, ta soma wannan sana’a ne da jarin kasa da 3,000, amma a yanzu sana’ar ta bunkasa da kuma fa’idar da take samu ta kai matsayin da ita da iyalinta gaba daya sun dogara a kai, kuma suna samun rufin asiri.

“Ban taba zaton za ta kai ga wannan matsayi ba. Saboda da ‘yan mudu kadan na fara, amma yanzu ga shi ina iya sayen buhunhuna in soya, in kuma sayar wa mutane da yawa daga wurare dabandaban.”

Mary ba fara kadai take sayarwa ba a inda take sana’arta, domin kuwa ta hada da kifi a gefe.

Da aka tambaye ta dalilin yin haka, sai ta ce, ta yi hakan ne saboda sha’anin kasuwanci, domin akwai lokacin da fara kan yanke.

“Da zarar mun shiga watan Yuli zuwa watan Agusta, a kan rasa farar baki dayanta, ni kuma ba zan so a ce na durkushe ba, shi ya sa na kasa kifi.

“Idan babu wannan, ga wannan. Da haka sai in yi kasuwancina tsawon shekara ba tare da ya tsaya ba, kuma hakan ya samar min da karin riba” in ji Mary.

Wata mai irin wannan sana’a mai suna Rakiya ‘yar Barno wacce ta ce, ta kwashe shekara uku tana yi, inda ta bayyana yadda take sarrafa danyar Farar, daga lokacin da ta sayo ta daga wadanda suka kamo, har ta kai ta kasuwa zuwa ga musu saye.

“Bayan mun sayo farar, sai mu wanke ta da ruwan zafi a gida, mu kuma sa mata kayan hadi da kayan kamshi da gishiri da kuma garin tafarnuwa, sai mu shanya ta a rana kafin mu soya ta.

“Mukan kuma soya ta soyu sosai ta yi marau. Sai kuma mu barbade ta da yaji, wanda muka yi masa hadi da kayan dandano domin karin armashi” inji Rakiya.

Wannan harka ta kamun fara na samar kudin shiga ga mutane da yawa, wanda hakan ya sa masu yin ta samun damar kula da iyalansu duk da barazanar Boko Haram da ta addabi yankin.

Sana’ar sayar da soyayyiyar fara na kara samun farin jini a hankali a ciki da kuma wajen Najeriya, wanda hakan ya haifar da bukatar a inganta sana’ar, tun daga yadda ake samar da farar da sarrafa ta, har zuwa ga yadda ake sayar da ita ga masu bukata musamman a Maiduguri.

Ba don komai ba, sai don cin fara ya zama hantsi leka gidan kowa a ciki da wajen jihar saboda samar da sinadarin furotin mai kara lafiya a madadin kifi da nama da kuma madara wadanda a yanzu sun fi karfin talaka la’akari da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.

Bugu da kari, Hukumr Kula da Harkar Noma da kuma Inganta Cimaka ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, fara na dauke da sindaren furotin da Bitamin da Faiba da kuma Ma’adinai masu gina jiki wanda sakamakon binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa, cin irin wadannn kwari marasa illa, yana da alfanu ga lafiya.