✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda shan Zobo yake kara lafiyar Zuciya

Bincike ya gano cewa shan Zobo na rage hatsarin kamuwa da cutar hawan jini

Wani bincike na shekarar 2010 da aka wallafa a mujallar nazari kan abinci masu gina jiki, ya gano cewa yawaita shan Zobo wanda a kimiyyance ake kira Hibiscus Sabdariffa, yana rage hatsarin kamuwa da cutar hawan jini.

Zobo ya kunshi wasu sunadarai da ke taimakawa wajen sanya nutsuwa a jijiyoyin da ke kai-komo da jini a jikin mutanen da ke daf da kamuwa ko fama da cutar hawan jini marar karfi.

Zobo yana rage yawan daskararren maiko wato Cholesterol a jikin masu ta’ammali da shi da wadanda suka mayar da shi abin shansu domin kuwa shi Cholesterol yakan lullube zuciya ce ya hana ta aiki yadda ya dace.

Wani bincike da aka wallafa a ‘Fitoterapia’, wata mujallar tsirrai na magunguna da kuma sanin asalinsu, ya tabbatar da ingataccen tasirin Zobo wajen magance cutar hawan jini.

Bugu da kari, binciken ya bayar da rahoton kyakkyawan sakamako dangane da yadda Zobo yake wargaza kudindinewar da Cholesterol yake yi a jikin zuciya.