✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda shugaban makaranta ya kashe ’yar shekara biyar ya binne gawarta a Kano

An cafke shugaban wata makarantar Firamare ta Noble Kids Nursery and Primary School bisa zargin kisan wata dalibarsa ’yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubakar.…

An cafke shugaban wata makarantar Firamare ta Noble Kids Nursery and Primary School bisa zargin kisan wata dalibarsa ’yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubakar.

Tun a watan Disambar bara ne dai rahotanni suka bulla cewa an dauke Hanifa a yankin Kawaji da ke Unguwar Yan Kaba a birnin Dabo.

Bayanai sun ce an sace dalibar ce a kan hanyar komawa gida bayan tashi daga wata makarantar Islamiyya tare da sauran dalibai.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an dai yi awon gaba da ita ce a cikin wani babur mai kafa uku da aka fi sani da A daidaita sahu.

Rahoton sace Hanifa dai ya tashi hankalin jama’a a Jihar Kano da kewaye, lamarin da ya sanya mutane suka shiga taitayinsu wurin yin taka tsan-tsan da daukar matakan tsaro.

Bayan sace ta ne Shugaban makarantar da ake zargi da wannan aika-aika mai suna Abdulmalik Tanko, ya nemi iyayenta su biya Naira miliyan shida a matsayin kudin fansarta.

Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar da ake zargi da sace Hanifa

A cewar wata Wasila Dahiru, an kama mutumin da ake zargi ne a ranar Laraba yayin da yake kokarin karbar wani kaso daga cikin kudin fansar da ya nema.

Sai dai ana haka ne dubunsa ta cika, inda ta kai ga an gano gawar Hanifa da aka daddatsa sassan jikinta kuma aka binne ta a harabar makarantar ta Noble Kid da ke Unguwar Tudun Wada.

Da yake tsokaci a kan lamarin, mai magana da yawun rundunar ’yan sanda Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa manema labarai a ranar da aka gano gawar cewa, jim kadan bayan sace Hanifa sai barayin suka kira iyayenta suna neman kudin fansa har kimanin naira miliyan shida.

Bayan samun rahoton ne sai kwamishinan ’yan sanda na jihar CP Sama’ila ya hada taron gaggawa na manyan shugabannin tsaro don gano yarinyar da kuma tumke damararsu a kan dabarun tabbatar da tsaro a Jihar Kano.

Daga nan kuma sai rundunar ’yan sanda ta tayar da tawagar Kan Ka ce Kwabo, wato Operation Puff Ader don tabbatar da kamo wadanda suka sace yarinyar.

“Da aka ci gaba da bibiya aka yi ta aiki da har nasara ta kai aka kama mutum biyu da farko, wato Abdulmalik Muhammad Tanko mai shekara 30 da abokinsa Hashim Isiyaku mai shekara 37 da suke unguwar Tudun Murtala, kuma jami’an DSS suka yi nasarar kama su,” inji DSP Abdullahi Haruna Kiyawa.

“Daga binciken da aka fara ne Abdulmalik ya tabbatar da cewa Hanifa dalibarsa ce tana karatu a makarantar da yake koyarwa a Kwanar Dakata. Ya sace ta ne ya kai ta gidansa ya boye ta har kimanin sati biyu, ya kuma nemi a ba shi kudi har naira miliyan shida.

“Ranar 18 ga watan 12 da ya fahimci ana so a gano cewa yarinyar tana tare da shi, don har gidansa ana ta bibiya an je, sai ya gaya mana (’yan sanda) cewa ya ba ta guba ta sha ta mutu.

“Daga nan sai suka hada baki da wancan abokin nasa Hashim suka dauke ta suka sa a buhu suka kai ta wannan makarantar suka yi tono suka binne ta,” kamar yadda kakakin ’yan sanda ya ce.

DSP Kiyawa ya kara da cewa “sai a yau 20 ga watan Janairun 2021 ne muka yi nasarar kamo su.”

Kakakin ’yan sanda ya ce sun fara da yi wa Hashim tambayoyi ne inda ya tabbatar da cewa hakika Abdulmalik ya neme shi ya taya shi wani aiki cewa akwai abin da za su je su binne a buhu, kuma ya taimaka masa wajen yin tonon a cikin makarantar suka kuma binne.

Sannan ya gaya wa ’yan sanda cewa kafin ma wannan lokacin shi Abdulmalik din ya samu Hashim shi da wata Fatima Jibrin Musa mai shekara 27 da ke zaune a Tudun Murtala, ya kuma ce musu su je su sato masa wannan yarinya, amma sun ce daga baya sun gaya masa ba za su yi ba.

A yanzu dai ’yan sandan sun ce dukkan mutum ukun da Abdulmalik da Hashim da Fatima duk suna hannun ’yan sanda za a ci gaba da bincike.