✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda siyasa take hana Kano ci gaba

Wani abu da ke kara ruruta wannan wuta shi ne dabi’un magoya baya.

A kwanakin bayan ne aka yi ta yamadidi da wani labari a Jihar Kano cewa wani dan Majalisar Tarayya ya kawo wani aikin ci gaba amma aka dakile shi, saboda abin da wadansu suka alakanta shi da bambancin siyasa.

Ana cikin haka sai ga wani abu da ya zame wa mutanen Kano abin sha’awa, wato zuwan tsofaffin gwamnonin Jihar Nasarawa, Kano a cikin jirgi daya don yin ta’aziyya.

Shin me ya sa wannan abu ya zama bambarakwai a Kano? Shin sabani a tsakanin jagororin siyasar Kano yana da tasiri wajen ci gaban jihar?

Aminiya ta tuntubi masana don jin ta bakinsu.

Shehun Malami a Sashin Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya bayyana cewa babu shakka babu hadin kai a tsakanin tsofaffin gwamnonin Jihar Kano, kuma wannan a fili yake ganin yadda suke zafafa siyasa a junansu ciki har da musayar yawu a kafafen yada labarai.

Kuma ya ce wannan yana kawo babbar illa ga ci gaban jihar, kuma wannan ya faru ne saboda yadda ’yan siyasa suke fifita bukatar kansu fiye da ta al’ummarsu.

Ya ba da misali da abin da yake faruwa a halin yanzu “Dubi irin alaka kyakkyawa da ta wakana tsakanin Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Kwankwaso, amma yanzu sun raba gari, ba sa ga maciji, sai hamayya da habaice-habaice a tsakininsu, abin da a wasu lokuta ke jawo tashe-tashen hankuali a tsakanin magoya bayansu, abin da kan kawo ci baya ta fuskar zaman lafiya a Kano,” inji masanin.

Ya ci gaba da cewa da wadannan shugabanni za su zauna su hada kansu su kawar da bambance-bambancen da ke tsakininsu, su fuskanci bunkasa Jihar Kano da an samu nasara mai yawa.

“Yanzu kalli a Kano Jam’iyyar APC mai mulki tana da tsofaffin gwamnoni har guda uku, ga Sanata Kabiru Gaya da Injiniya Rabi’u Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau.

“Idan suka hadu suka tafi Abuja suka ce ga bukatar jama’ar Kano, lallai za a ga kwarjininsu a yi musu wani abu a ciki.

“Yanzu dubi yadda Yarbawa suka ajiye bambancin siyasa suka hade wa Gwamnatin Tarayya baki lokacin da suka kirkiro dakarun tsaro na Amotekun,” inji Shehun Malamin.

Shi ma da yake yi wa jaridar Aminiya bayani a kan wannan batu, Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa na Jami’ar ta Bayero ya ce babban dalililn da ke jawo wannan sabani shi ne dagewa da wadansu tsofaffin gwamnonin suke yi na cewa dole su ci gaba da zama jagororin siyasa a jiharsu, bayan sun bar gwamnati.

“Idan ka dubi abin da ’yan siyasar Jihar Nasarawa suka yi ya faru ne saboda tsofaffin gwamnonin sun yarda cewa su tsofaffin gwamnoni ne.

“Sannan sun yarda wadanda suke kai jagorori ne.

“Bayan wannan, wani abu da ke kara ruruta wannan wuta shi ne dabi’un magoya baya, domin su ma suna da zafin kai, sun ki yarda a ce shugabanninsu ba su ne jagorori ba.

“Dole yadda suke jin su a lokacin da suke mulki haka suke so su ci gaba da zama, ba wanda zai wuce su,” inji shi.

Da masanin ya juya bangaren gwamnonin da ludayinsu ke kan dawo ya ce su ma suna da nasu laifin wajen hargitsa alaka a tsakaninsu da gwamnonin da suka shude.

Ya ce “Idan ka kalli gwamnonin jihohin Yarbawa alal misali, sun yarda cewa akwai dattijai a jihohinsu da suka hada da manyan sojoji da sarakunan gargajiya da malaman addini, wadanda ake sauraron shawarwarinsu ake mutunta maganganunsu.

Amma mu a nan da zarar Gwamna ya dare madafun iko shi ke nan ba wanda ya isa sai shi, ya raina kowa, ba ya ganin mutuncin malamai ko sarakunan gargajiya da manyan ’yan kasuwa, to wa kake zaton zai iya kokarin gyara alaka a tsakanin tsofaffin shugabanni idan ta baci, tunda Gwamna mai ci bai ba da kofar haka ba?”

Ya ce ba tsohon Gwamna ba, ko ma’aikacin gwamnati wanda ya yi biyayya ga tsohon Gwamna kamar yadda doka ta nemi ya yi, sai wata gwamnatin ta dauke shi a dan adawa, za a iya cire shi a nada wanda bai cancanta ba.

Ya ce har ta kai wadansu gwamnonin suna nada mutane a mukaman siyasa saboda kwarewarsu wajen hamayya da wani cikin tsofaffin gwamnoni.

Dokta Dukawa ya nanata muhimmncin samun hadin kai a tsakanin shugabanni don samun ci gaba mai dorewa.