✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji ke kula da tubabbun ‘yan Boko Haram

Rundunar hadin gwiwar kasashen masu yaki da Boko Haram a yankin Tabkin Chadi (MNJTF) ta yi alkawarin cikakkiyar kula ga mayakan kungiyar da suka mika…

Rundunar hadin gwiwar kasashen masu yaki da Boko Haram a yankin Tabkin Chadi (MNJTF) ta yi alkawarin cikakkiyar kula ga mayakan kungiyar da suka mika wuya a baya-bayan nan.

Kwamandan NMJTF Manjo Janar Ibrahim Yusuf, ya bayar da tabbacin a jawabinsa ga tsoffin mayakan a yankin Arewa mai zurfi na kasar Kamaru.

Ya bukace wadanda suka mika wuyan su ba wa tsoffin abokansu shawara su fito daga jeji su mika wuya ga gwamnati, domin babu abin da za a yi musu.

Janar Ibrahim ce akidar kungiyar gurbatacciya ce da wasu batattu suka kawo domin jefa miliyoyin jama’a cikin bala’i a yankin domin biyan bukatunsu.

Ya ce kowace kasa da rikicin Boko Haram/ISWAP ya shafa ta bullo da tsarinta na kawo karshen matsalar ta hanyar karbar makamai da sauya halayyar tsoffin mayaka da kuma sake shigo da su cikin al’umma.

Da yake jawabi, kakakin wadanda suka mika wuyan ya yaba wa gwamnati kan yadda ta karbe su hannu biyu take kuma kula da su da iyalansu.

Ya ce dukkansu da suka mika wuya suna cikin koshin lafiya sabanin yadda shugabannin kungiyar ke cewa za a kashe su idan suka mika wuya.

“Amma ga mu nan ana kula da mu kamar mutane”, inji shi.

Ya roki gafara tare da bayyana nadamar abubuwan da suka aikata a lokacin da suke cikin kungiyar.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Kakakin MNJTF, Kanar Timothy Antigha, ya fitar a birnin N’Djamena na kasar Chadi.