✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji suka gudanar da Musabakar Al-Kur’ani a Borno

Sojoji sun karrama gwaron musabakar da kyautar kujerar Umrah

Rundunar Operation Hadin Kai ta sojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram ta gudanar da gasar karatun Al-Kur’ani ta matasa a yankin Monguna na Jihar Borno.

Muhammad-Nur Mustapha, wanda ya zama gwarzon gasar, ya samu karramawa da kyautar kujerar zuwa aikin Umrah.

Wanda ya zo na biyu kuma, Zaharadeen Yusuf ya samu kyautar kudi N300,000 sai Mohammed Ali  da ya zo na uku da aka ba wa kyautar kudi N200,000. Sauran wadanda suka samu karrmawa sun hada da wanda ya fi iya kira’a da dai suransu.

Babban Limamin Monguno, Alhaji Liman Kaumi, ya jagoranci malamai wajen halartar ta musabakar Al-Kur’ani da sojojin suka shirya, a yayin da Ajiyan Monguno, Alhaji Zanna Bulama, ya jagorinci sarakuna zuwa taron.

A jawabinsa na bude musabakar, mai masaukin baki kuma Kwamandan Runduna ta 111, Manjo-Janar A.E Abubakar, ya ce gasar za ta taimaka wajen samun nasara a yaki da ta’addan ba tare da amfani da karfin soji ba.

Ya bayyana cewa Babban Kwamandan rundunar, Manjo-Janar I.S Alkali, ya kirkiro ya kuma dauki nauyin gasar karatun Al-Kur’anin ne da nufin ganin al’umma sun samu karin kusanci da Allah da kuma cusa wa mutanen yankin kaunar sojoji.

Manjo-Janar I.S. Ali, ya ce musabakar za ta kara dora matasa a turbar da za su fahimci addinin Musulunci yadda ya kamata da kuma wanzar da zaman lafiya.

Don haka ya bukaci samun karin hadin kai daga masu ruwa da tsaki domin tabbatuwar zaman a fadin Jihar Borno.

Kakakin rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya bayyana cewa shirya musabakar wata hanya ce ta kara kyautata alaka da karfafa hadin kan da sojoji ke samu daga al’ummar wajen yaki da ta’addanci.

A sakonsa ga taron, Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulumi, wanda Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Monguno, ya wakilta, ya jinjina wa sojojin bisa shirya musabakar da kuma nasarorin da suke samu a yaki da ta’addanci ba ta hanyar soji ba.

Ya kuma nuna godiyarsa bisa tabbacin da ya samu daga Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya wajen ci gaba da murkushe ayyukan ta’addanci a fadin jihar.