✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji suka kashe Kachalla Gudau —Aruwan

Gudau ya taka muhimmiyar rawa a garkuwa da dalibai da ’yan kasashen waje.

Dakarun Soji sun yi nasarar kashe Kachalla Gudau, daya daga cikin kasurguman ‘yan fashin daji da suka addabi yankunan Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya sanar da wannan galaba da sojojin kasar suka samu wacce ta yi sanadin mutuwar Kachalla Gudau.

A cewar Aruwan, “Kasurgumin dan bindigar nan Kachalla Gudau, wanda ke jagorantar gungun ‘yan fashin daji wajen yin garkuwa da mutane da kisa a kananan hukumomin Chikun, Kachia, da Kajuru, na daya daga cikin ‘yan fashin dajin da dakarun Najeriya suka kashe a ranar Lahadi a Kankomi da ke Jihar Kaduna.”

Gudau a cewar sanarwar, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da suka kai wani hari a yankin Kankomi, harin da sojojin Najeriya suka dakile suka fatattaki ’yan bindigar har ya kai ga mutuwarsa.

“An tsinci gawarsa [Gudau] a dajin Kankomi, wanda bisa ga dukkan alamu, ya mutu ne saboda yawan jinin da ya zubar.

“Sahihan bayanai sun yi nuni da cewa, bayan da ’yan uwansa ’yan fashin daji suka dauko gawarsa, sun yi jana’izarsa a yankin Dajin Kaku da ke Kaso a karamar hukumar Chikun.”

Kazalika wannan harin da dakarun suka dakile, ya yi sanadin mutuwar wani “aminin” Gudau da ake kira “Rigimamme”.

Gudau ya taka muhimmiyar rawa a garkuwa da dalibai da ’yan kasashen waje a kananan hukumomin Kajuru, Chikun da Kachia a jihar ta Kaduna.