✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji suka ragargaji Turji da yaransa a Sakkwato

Babban Kwamanda na Runduna ta 8 ta Sojin Kasa ta Najeriya da kansa ya jagoranci harin

Sojoji sun kashe ’yan bindiga da dama a musayar wuta da suka yi da yaran hatsabibin dan bindigar nan Bello Turji a Jihar Sakkwato.

Yaran na Bello Turji sun gamu da ajalinsu ne a kauyukan Katanga da Satiru, bayan Babban Kwamanda (GOC) na Runduna ta 8 ta Sojin Kasa ta Najeriya ya jagoranci sojoji sun yi bi su har kauyukan sun yi musu kofar rago a ranar Alhamis.

Wani dan sa-kai da ke tare da sojoji a lokacin harin ya ce, “A akalla motoci 20 ne suka yi wa wurin dirar mikiya, mun dauki awanni muna musayar wuta da su; In takaita maka bayani, har sai da jirgin yaki ya kawo dauki muka fatattake su suka ja baya.

“Zuwa yanzu da wuya a iya tantance yawan wadanda muka kashe, amma ba a kashe mana ko mutum daya ba. Mun samu nasara,”

Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa baya kauyukan Katanga da Satiru na hanun Turji da yaransa, suna cin karensu babu babbaka.

Wani mazaunin garin Isa ya shaida wa wakilinmu cewa a lokacin da ake ba-ta-kashin, sun ga dandazon ’yan bindiga na zuwa wurin domin mara da ’yan uwansu baya.

“Amma bayanan da muka samu sun nuna sun kwashi kashinsu a hannun sojoji; Yanzu haka GOC da dakarunsa na bin daji suna share ’yan bindigar a maboyansu,” a cewarsa.

Wata majiyar soji ta ce GOC din ya lashi takobi cewa ba zai kowa gida ba sai sun gama fatattakar ’yan bindiga daga yankin Gabashin Jihar Sakkwato.

“Jajirtacce ne kuma ba ya son duk abin da zai kawo nakasu, shi da kanshi yake jagorantar sojoji a daji,” inji majiyar.