✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji suka ragargaza ’yan Boko Haram a Borno

Mayakan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannun sojojin Najeriya

Dakarun sojin Najeriya da sun ragargaza mayakan Boko Harma da suka kai hari a garin Marte, Jihar Borno.

Maharan da suka kwashi kashinsu hannun sojojin da suka yi musu kofar rago, sun kai harin ne kimanin wata guda bayan komawar mutanen garin gidajensu daga gudun hijirar da suka yi na shekara shida a Jamhuriyar.

Mukaddashih Daraktan Yada Labaran Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Birgediya Bernard Onyeuko, ya ce dakarun rundunar Operation Tura Takaibango da jiragen yakin Rundunar Operation Lafiya Dole “sun tarwatsa motocin yaki bakwai na Boko Haram a lokacin da suke yunkurin kai wa sansanin sojin hari a Marte.

“Bayan samun rahoton harin, sai sojojin suka janye, suka yi wa mayakan kwanto a wani wuri, inda suka jira maharan suka kuma bude musu wutar da ta kai ga nasarar, ” inji sanarwar ta ranar Asabar.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda sojojin suka yi fata-fata da mayakan Boko Haram din.

Boko
Wata daga cikin motocin yakin Boko Haram da sojoji suka yi raga raga da ita
Boko Haram
Wasu motocin sojoji da suka bi sawun mayakan suka kuma hallaka su a Marte.
Boko Haram
Yadda wata daga cikin motocin Boko Haram din ta yi kaca-kaca baya ta sha ruwan wuta
Boko Haram
Wata motar Boko Haram da ta kone bayan sojojin Najeriya sun yi mata luguden wuta
Boko Haram
Motar mayakan da sojoji suka hallaka a Marte, Jihar Borno
Yadda wata daga cikin motocin mayakan ta kone kurmus bayan sojoji sun yi musu kofar rago.