✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojojin Faransa suka taka bam a Burkina Faso

Dakarun sojin sun taka bam din a yayin da suke sintiri.

Akalla dakarun sojin kasar Faransa hudu ne suka jikkata a Arewacin kasar Burkina Faso bayan motarsu ta taka bam.

Tashin bam din ya tarwatsa motar sojojin ne bayan ta fito daga filin jiragen saman Ouahigouya kamar yadda rundunar sojin ta Faransa ta bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin da hatsarin ya rutsa da su na rundunar yaki da ’yan ta’adda ta  Barkhane ne da ke aikin sintiri a yankin.

An garzaya da sojin da suka ji rauni zuwa asibiti a birnin Gao na kasar, wadanda kuma rauninsu ya kazanta za a  garzaya da su Faransa don ba su kulawar da ta dace.

Yankin na fama da hare-haren ’yan ta’addan JNIM, GSIM wadanda dukkaninsu wani tsagi ne na kungiyar Al-Qaida.

Tun a 2014 aka girke dakarun sojin Barkhane a kasar Mali, daga baya kuma ya fadada zuwa Burkina Faso, da yankin Sahel don yin sasanci musamman ga al’amuran da suka shafi siyasa da diflomasiyya.