✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojojin Mali suka yi wa fararen hula 71 kisan gilla —Rahoton HRW

Human Rights Watch na zargin sojojin Mali da kin ba a bai wa wadanda ake zargi damar kare kansu.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch ta zargi sojojin kasar Mali da yi wa fararen hula sama da 71 kisan gilla a cikin wata hudu da sunan yaki da ’yan ta’adda.

Kungiyar ta ce sojojin sun kashe yawancin mutanen ne daga farkon watan Disamba 2021 zuwa yanzu, ba tare da ba su damar kare kansu daga tuhumar da ake musu ba.

Kungiyar da ta ce ta tattara bayananta ne daga shaidu mutum 49, ta bayyana cewa yadda sojojin Malin ke yaki da ’yan ta’adda ya saba da doka, duba da yadda suke yi wa fararen hula hawan-kawara.

Human Rights Watch na zargin sojojin da rashin gudanar da bincike yadda ya kamata tare da kafa hujja kafin zartar wa mutanen da aka kama da laifi hukunci.

Sai dai tuni gwamnatin mulkin sojin Mali ta yi watsi da wadannan alkaluma da kungiyar ta fitar a cikin wani sabon rahotonta.

An dai shafe tsawon lokaci hukumomin kare hakkin dan na zargin sojojin Mali da cin zarafin mutane yayin yaki da ’yan ta’adda.

Amma gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojin Mali da ta kafu bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a 2020, ta ci gaba da musanta zarge-zargen.