✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ta kaya a manyan wasannin Firimiyar Ingila ranar Asabar

Arsenal ta yi wa saman teburin gasar Firmiyar Ingila zaman dabaro.

A wannan Asabar aka soma wasannin mako na shida na Firimiyar Ingila wadda a halin yanzu Arsenal ta yi wa saman teburin gasar zaman dabaro.

Liverpool da Everton ne suka bude taro da wasan da aka fafata a Goodison Park wanda suka raba maki bayan an tashi canjarasa marar ci.

Chelsea da West Ham United

Ita kuwa Chelsea doke West Ham ta yi da ci 2-1 a wasan da suka buga a Stamford Bridge.

West Ham ce ta fara cin kwallo ta hannun Michail Antoni a zagaye na biyu, bayan da suka tashi ba shi a minti 45 din farko.

Kwallon farko kenan da Antonio ya ci wa West Ham a Premier a kakar nan, bayan buga aka yi wasa shiga da fara kakar bana.

Daga baya Chelsea ta farke ta hannun Ben Chilwell, sannn Kai Havertz ya kara na biyu saura mini biyu a tashi daga karawar.

Wannan shi ne wasa na 18 da David Moyes ya je Stamford Bridge amma bai yi nasara ba.

Fulham da Tottenham

Tottenham ta yi wasa shida ba tare da rashin nasara ba, bayan da ta doke Fulham 2-1 a wasan mako na shida da suka kara a Asabar din.

Pierre-Emile Hojbjerg ne ya fara ci wa Tottenham kwallo na biyu da ya zura a raga a kakar nan.

Harry Kane ne ya kara na biyu a minti na 75, kwallo na biyar da ya ci kenan a kakar Firimiyar Ingila da ake bugawa.

Saura minti 10 a tashi Fulham ta zare daya ta hannun Alexander Mitrovic a wasa na biyu da Marco Silva ya yi rashin nasara a kakar nan.

Manchester City da Aston Villa

Aston Villa da Manchester City sun raba maki a wasan mako na shida a gasar Firimiyar da suka fafata a Villa Park.

Manchester City ta fara cin kwallo minti biyar da komawa zagaye na biyu ta hannun Erling Haaland.

Saura minti 16 su tashi daga wasan ne Villa ta farke ta hannun Leon Bailey, hakan ya sa suka raba maki a tsakaninsu.

Wannan dai shi ne kwallo na 10 da Halaand ya zura a raga a wasa shida da fara kakar nan, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a Firimiyar a bana.

Wanda yake da tarihin cin 10 a wasan Firimiyar a wasa shida da fara gasar shi ne Mick Qumn na Coventry a 1992.

A ranar Lahadi ce Manchester United za ta karbi bakuncin Arsenal a Old Trafford.