✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Tafiyar awa 2 ta dauke su wata 7 a Jirgi

Rashin tsaro da lalacewar hanya ta sa mutane da dama suka kaurace wa bin hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda a wasu lokutan ake kallon masu…

A ranar 28 ga Maris na bana, wasu mutane suka taso daga Abuja da zummar zuwa Kaduna, tafiyar ba ta wuce biyu da rabi ba, amma kash! Sai da suka yi wata bakwai.

Rashin tsaro da lalacewar hanya ta sa mutane da dama suka kaurace wa bin hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda a wasu lokutan ake kallon masu bin hanyar a matsayin masu kasada.

A wannan ranar ta 28 ga Maris, iyalai da ’yan uwa da abokan arziki sun yi wasu da ’yan uwansu da suka taso daga Abuja, wasu ziyara za su zo, wasu gida za su dawo, wasu kuma aiki za su je.

Hakan ya sa motoci da babura suka taru a Tashar Jirgin Kasa da ke Rigasa da ke Kaduna suna tsimayin karasowar ’yan uwansu.

Fasinjojin sun taso ne da niyyar tafiyar awa biyu da, ashe za su yi tafiya ne mafi ‘nisa’ a rayuwarsu, inda ba su sani ba, ashe wasu daga cikinsu za su kasance a hanyar Kaduna zuwa Abuja na wata shida.

A ranar, a daidai lokacin da mutanen suke jira, sai ga labari da dumi-diminsa, ’yan ta’adda sun tare jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, sun kashe mutane da dama sun kwashe wasu.

Washegari aka tabbatar da wadanda aka kashe, sauran kuma aka fara jiran dawowarsu.

Daga nan ne jiran da suke tunanin za su yi na ’yan mintuna, sai ya koma awanni, daga nan ya koma na kwanaki.

Tun ana tunanin kwanaki, sai aka koma makonni, har a kwana a tashi ya kai sama da rabin shekara.

Duk da yake an sako mutum daya a makon da abin ya faru mai suna Alwal Hassan, wanda rahotanni suka ce sai da aka biya Naira miliyan 100, daga lokacin aka rika yin fansar mutanen kadan-kadan, har zuwa ranar Laraba da Gwamnatin Tarayya ta kubutar da sauran.

Shigar Tukur Mamu tsakani

Ana cikin haka ne, sai dan jarida, Tukur Mamu ya fara shiga tsakanin gwamnati da ’yan bindigar, inda da farko ya sanar da cewa ’yan bindigar suna bukatar a sako musu ’ya’yansu da wasu kwamandojinsu kafin su sako mutanen.

Da wannan ya ci tura, sai Mamu ya fara shiga tsakanin iyalan wadanda aka sace din da ’yan ta’adda, inda ya yi sanadiyar dawowar mutane da dama.

Sai dai su ma rahotanni sun nuna cewa sai da suka biya miliyoyin Naira da daloli da aka kiyasta sun kai Naira biliyan biyu.

Daga nan ne aka bar wadanda ba su da ikon biyan makudan kudaden nan a cikin daji, suna neman agaji daga Allah da kuma gwamnati.

Ana cikin haka ne kuma gwamnati ta kama Tukur Mamu, tana zargin sa da hannu a cikin lamarin, duk da ya karyata zargin, amma dai ana kotu.

Ana cikin haka ne kwatsam, sai Gwamnatin Tarayya ta sanar da ta samu nasarar kubutar da sauran fasinjojin da suka rage, karkashin jagorancin kwamitin da Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Leo Irabor ya kafa.