✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda takarar ministoci ke shafar ayyuka a ma’aikatun gwamnati

Binciken Aminiya ya gano harkokin gwamnati sun fara na tafiyar hawainiya a ma'aikatun da wasu masu wannan buri ke jagoranta.

A yayin da ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati da ke neman takara a zaben 2023 suka fara yawon kamfe, binciken Aminiya ya gano harkokin gwamnati sun fara na tafiyar hawainiya a ma’aikatun da wasu masu wannan buri ke jagoranta.

Kasa da mako uku da fara gudanar da zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC mai mulki,  har yanzu ministoci da wasu masu rike da mukaman siyasa da suka fito takara ba su ajiye mukamansu ba.

Kawo yanzu, minsitoci da suarn masu neman takarar sun dukufa yawon neman goyon baya da kuri’un daliget domin su samu zama ’yan takara a zaben na 2023.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da ministoci masu neman kujerar shguaban kasa irin su Rotimi Amaechi da Chris Ngige da dai sauransu, na daga cikin masu irin wadannan tafiye-tafiye zuwa sassan kasar nan domin zawarcin deliget da sauran masu ruw da tsaki.

Sauran ministoci masu neman tsayawa takarar shugaban kasa sun hada da Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu; da Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Timpre Sylva; da kuma Minista a Ma’aikatar Ilimi, Chukeuemeka Nwajiuba.

Shi ma Gwamnan Babban Banki Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wanda ya yi karar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da Babban Lauyan GwamnatiN Tarayya, Abubakar Malami kan kokarin hana shi tsayawa takarar ba tare da ya ajiye aikinsa ba.

Binciken Aminiya ya gano cewa shi ma Malami yana cikin masu neman magoya bayan da za su zabe shi, amma a matsayin Gwamnan Jihar Kebbi.

Jam’iyyar APC dai ta ware ranar 30 zuwa 31 ga watan Mayun da muke ciki a matsayin ranakun gudanar da zabenta na fitar ’yan takarar shugaban kasa.

Zuwa yanzu dai akalla ’yan takara 30 ne suka sayi fom din takarar shugaban kasa a jam’iyyar, kowannensu a kan Naira milyan 10o.

Daliget 7,800 daga sassan kasar nan ne ake sa ran za su jefa kuri’a domin zabar dan takarar shugaban kasar APC a babban zabe mai zuwa na 2023.

An ruwaito cewar gabanin zaben, ’yan neman takarar suna zuwa jiha-jiha domin saye zukatan daliget din da za su jefa kuri’a a ranar zaben.

A bangare guda kuma masu hasashe sun bayyana cewa mayar da hankali a kan kamfe da masu neman maye gurbin Shugaba Buhari a zabe mai zuwa ke yi ya kawo koma baya a harkokin gwamnati.

An samu cikas a Ma’aikatar Kwadago

Bincike da Aminiya ya gano cewa tun lokacin da Ministan Kwadago da Ingantuwar Aiki, Chris Ngige, ya fito ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa aka  ayyuka suka fara tabarbarewa a ma’aikatar.

Wani ma’aikacin hukumar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa tun lokacin da ministan ya sanar da aniyarsa ta neman shugabanci ayyuka suka yi ta komawa baya saboda.

A cewarsa, yanzu haka akwai takardun da ke neman a rattaba hannu a kansu, amma sabado ba ya zama ba a yi komai a kansu ba.

Na baya-bayan nan ma shi ne na yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) domin kuwa an bayyana cewa tun lokacin da kungiyar ta shiga yajin aiki, duka bai fi zama biyu ya yi da su ba, a matsayinsa na ja-gaba mai shiga tsakanin kungiyar da gwamnati.

Abun da ya haifar da haka kuwa shi ne yanzu ba ya zama yana can yana neman goyon baya daga jihohi daban-daban.

Amaechi: Mai jifar tsuntsu biyu da dutse daya

A lokacin da Amaechi ya bayyana aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa an misilta shi da mai jifar tsuntsu biyu da dutse daya.

Ana ganin yana amfani da ayyukan da ma’aikatarsa ke yi ta hanyar ziyartar wuraren da ake gudanar da ayyuka domin neman magoya baya.

A ’yan kwanakin da suka gabata, ya je duba aikin da ake yi na layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri, daga nan kuma ya wuce zuwa Kano inda ya yi wata ganawa da Sarkin Kano da kuma Sarkin Bichi a ranar Litinin.

Ya kuma duba aikin layin dogon da ya taso daga Kano zuwa Kaduna, daga nan ya wuce Jigawa inda ya gana da Sarkin Dutse, sannan ya wuce ya ga Sarkin Daura domin zagawa ya ga wasu ayyukka.

Bincikenmu ya gano cewa a yanzu haka, Minista a Ma’aikatar Sufuri, Sanata Gbemisola Saraki, ita ce ke zuwa ma’aikatar domin maye gurbinsa.

Ministan Kimiyya da Fasaha

Da yake shi bai jima da bayyana aniyarsa ba, Ministan Kimiyya da Fasaha, Dokta Ogbonnaya Onu, an ce ya je ofis a ranar Litinin kuma yana aikinsa.

Wani wanda wakilinmu ya samu zantawa da shi da ya nemi a boye sunansa ya ce abubuwa suna tafiya daidai a ma’aikatar ta kimiyya da Fasaha da Dokta Onu ke jagoranta.

Duk da haka, ya bayyana cewa ya san nan ba da jimawa ba shi ma zai fara tafiye-tafiye domin neman goyon baya.

Nwajiuba, Ministan Ilimi

Kokarin wakilinmu ya ci tura wajen gano irin kamun ludayin Minista a Ma’aikatar Ilimi, Emeka Nwajuiba bayan ya bayyaana aniyarsa ta takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Amma Daraktan Yada Labaran Ma’aiakatar Ilimi ta Tarayya, Ben Goong, ya ce Nwajibu na yin aikinsa.

Emefiele: Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Mun yi kokarin samun ma’aikatan CBN da su yi magana a kan yadda harkoki ke tafiya a bankin bayan Gwaman bankin Godwin Emefiele ya fito takarar shugaban kasa,  sai dai sun ce ba huruminsu ba ne don haka ba za su ce komai ba.

Amma wani babban jami’i a bankin ya bayyana cewa aniyar da Mista Emefiele ya bayyana ta neman takarar shugaban kasa ba ta shafi aikin babban bankin ba, don haka wannan bai zama wani abun damuwa ba a gare su da kuma bankin.

Idan za a iya tunawa dai, wata kungiya ce ta yi ikirarin saya wa gwamnan babban bankin fom na Naira milyan 100 domin tsayawa takara.

Daga bisani ya fito ya yi watsi da shi, inda ya yi ikrarin ba ya bukatar wani ya saya masa fom din takara, idan ya tashi zai saya da kudinsa.

‘Muna bukatar kwararan dokoki’

Wani masanin shari’a, Ibrahim Yusuf Habibu, ya ce karan tsayen da wasu masu wata manufa suka yi wa Dokar Zabe to 2022 da Shugaba Buhari ya sanya wa hannu ta bude wata kofa ta wucin-gadi ga masu rike da mukaman siyasa.

Sashe na 84(12) na dokar yaben ya bayyana cewa wajibi ne duk masu rike da mukaman siyasa – ministoci, kwamishinoni, mashawarta da sauransu – su ajiye mukamansu kafin su iya shiga harkar zabe a matsayin ’yan takara ko daliget.

Amma daga baya a ranar 18 ga watan Maris, 2022, Babbar Kotun Tarayay da ke zamanta a Umuahia, Jihar Abia, ta soke shashen bisa hujjar cewa yana karo da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

Majalisar Dattawa ta daukaka kara saboda rashin gamsuwa da hukuncin kotun.

Gwamnati ta ‘durkushe’ — Kari

Masanin Kimiyyar Siyasa kuma malami a Jami’ar Abuja, Dokta Abubakar Umar Kari, ya ce abin takaici ne yadda masu mukaman siyasa suka ci gaba da zama a kan mukaman alhali suna takara.

“Hausawa sun ce ‘Ba a tauna taura biyu,’ saboda haka babu yadda za a yi su iya gudanar da aikinsu na gwamnati mai tattare da nauyi mai yawa yadda ya kamata, sannan su hada da cukucukun siyasa.

“Ko suna ganin doka ba ta wajabta musu sauka da mukaman nasu na gwamnati su mayar da hankali kan siyasa ba, ya kamata hankalinsu ya nuna musu cewa su sauka.

“Mafi ban haushin shi ne Shugaba Buhari ya bar su a kan mukaman nasu, wadda alama ce ta shiririta da rashin sanin ya kamata daga bangarensa.

“A takaice gwamnatinsa da durkushe, ko ta susuce, saboda manyan jami’an gwamantin sun yi watsi da aikin da aka ba su, sun mayar da hankali kan harkokin siyasarsu gadan-gadan.

“An yi watsi da gudanar da gwamnati, an bai wa siyasa muhimmanci fiye da komai, kuma wannan ba zai kai kasar nan ga tudun mun tsira ba,” inji Dokta Kari.

Daga Abubar Maccido, Ismail Mudashir, Sunday M. Ogwu, Zakariyya Adaramola, Idowu Isamotu, Chidimma C. Okeke (Abuja) & Abdullateef Aliyu (Legas)