✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Taliban ke yaki da shan miyagun kwayoyi a Afghanistan

Taliban ta lashi takobin raba kasar Afghanistan da matsalar shaye-shaye.

Tun bayan kafa gwamnatin Taliban na farko a kasar Afghanistan ta fara sa kafar wando daya da masu shan miyagun kwayoyi a kasar musamman a birnanen Kabul da Kandahar.

Afghanistan na daya daga cikin kasashen da ake noma tare da sarrafa nau’unka miyagun kwayoyi, wannan ya sa ake fama da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a kowane lungu da sakon kasar.

A yunkurin gwamnatin Taliban na dabbaka shari’ar Musulunci a kasar tashi haikan don dakatar da wannan mummunar dabi’a ta shaye-shaye.

Jami’an Taliban din sukan kai sumame a matattaran masu yan shaye-shaye, musamman a karkashin gadoji da wuraren zubar da bola.

Hoto: AP

A yayin kowane sumame sukan kama mutane da dama, su tsare su sannan daga baya a kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

Hoto: AP Hoton wasu daga cikin ‘yan shaye-shayen da Taliban din su ka kama

Ana ba wa mashayan kulawa ta musamman tare da ba su magani da kuma tabbatar da sun rabu da wannan dabi’a a ta shaye-shaye da tasirinta a jikinsu.

Akan tsare wadanda aka kama na tsawon kwana 45, a asibitin inda ake ba su da kulawa ta musamman domin ganin an raba su da dabi’ar ta shaye-shayen.

Yadda likitoci ke kula da wadanda aka kama a asibiti.

Wannan yaki da Taliban ke yi da ’yan kwayar yana fuskantar kalubale,  kasancewar asibitocin na fama da karancin magugunan jinyar masu fama da tasirin hodar heroin.

Ba iya kan mashayan Taliban din suka maida hankali ba,  hatta manoman wadannan kayan maye ba su tsira ba kamar yadda wani jami’in gwamnatin Taliban ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AP.

Kafar ta kara da cewa, ’yan kasar Afghanistan da dama sun dogara ne a kan harkallar miyagun kwayoyi wajen samun kudade kamar wani manomin tabar Mohammed Kabir mai shekara 30 ya bayyana wa AP a zantawar da ta yi da shi.

Yadda ake noma Poppy a Afghanistan

A wannan lokacin da Taliban ke yaki da shaye-shaye, masu harkallar na neman kayan da daga wurare daban-daban, sannan a watan Nuwamba ake girbe poppy, wanda ake amfani da shi wajen yin kwayoyi, kuma  noma ita ce kadai sana’ar manomanta, a cewar Mohammed.

Taliban ta yi alkawarin tabbatar da tsaro a Afghanistan ta hanyar daukar tsauraran matakai kan miyagun ayyuka da kuma fatattakar masu neman kawo musu cikas a abubuwan da suka sa a gaba.