✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda tankar mai ta yi bindiga ta kone gidaje da shaguna

Birki ya kwace wa tankar inda ta afka kan wasu shaguna da gidaje.

Wata tanka makare da man fetur ta kwace tare da afkawa kan wasu gine-gine a yankin Apata da ke birnin Ibadan, a Jihar Oyo.

Wani ganau ya ce shaguna da gidaje sun kone sakamakon gobarar da ta tashi bayan motar ta kwace a lokacin da ta fito daga yankin Titin NNPC, ta afka wa gine-ginen da ke kallon wani gidan man NNPC.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an samu cunkoson ababen hawa a Babbar Hanyar Ibadan zuwa Ibadan, bayarn faru da magaribar ranar Alhamis.

NAN ya ruwaito cewa abin ya faru ne a daidai Mahadar Apata daura da gidan man NNPC a kan babbar hanyar.

Sai dai har yanzu ba a kammala tantance adadin shaguna da gidajen da tankar ta yi sanadin konewarsu ba kuma babu rahoton mutuwa ko samun rauni a sanadin lamarin.

Tuni jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Ogun suka yi wa wajen tsinke inda suka kwana suna kokarin kashe wutar.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Olawale Osifeso, ya ce tuni suka tura karin jami’ansu zuwa yankin don tabbatar da doka da oda.