✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda taron Kungiyar Lauyoyi ya hada ’yan takarar Shugaban Kasa

Taron ya gudana ne ranar Litinin a Otel din Eko Hotels and Suites da ke yankin Victoria Island a Legas.

Jiga-jigan ’yan takarar Shugaban Kasa na manyan jam’iyyun Najeriya a babban zaben 2023, sun halarci taron shekara-shekara na  Kungiyar  Lauyoyi ta Najerita (NBA).

Taron wanda shi ne karo na 62 ya gudana ne ranar Litinin a Otel din Eko Hotels and Suites da ke yankin Victoria Island a Legas.

Mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ne ya soma bude taron da jawabi.

A bayyana taken taron na bana a matsayin taro mafi girma na Lauyoyi a doron kasa.

Babban Alkalin Jihar Legas, Mai shari’a Kassim Alogba da ya wakilci mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya CJN, ya yaba wa Shugaban Kungiyar NBA, Olumide Akpata bisa halayensa na jagoranci nagari.

Wadanda suka halarci bikin bude taron sun hada da: Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, kuma dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023. Sai Peter Obi, dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP da kuma Mataimakin Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Kashim Shettima.

Mataimakin Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Kashim Shettima
Dan takarar Shugaban Kasa na PDP, Atiku Abubakar
Mataimakin Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Kashim Shettima da Gwamnan Filato, Simon Lalong da wasu manyan baki
Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi