✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Thomas Partey zai gyara Arsenal a kakar bana

A daren ranar Litinin ta makon jiya, wato ranar da aka rufe hada-hadar ’yan wasa ce kungiyar Arsenal ta sayo dan wasan tsakiyan Atletico Madrid,…

A daren ranar Litinin ta makon jiya, wato ranar da aka rufe hada-hadar ’yan wasa ce kungiyar Arsenal ta sayo dan wasan tsakiyan Atletico Madrid, Thomas Partey, dan kasar Ghana.  

Arsenal ta biya Fam miliyan 45 ne domin sayo dan wasan, bayan turjiya da kai-komo da aka yi ta samu daga Atletico Madrid da kocinta, Diego Simeone wanda ya nuna rashin yarda a sayar wa Arsenal da dan wasan.

Rashin jin dadi kan sayar da dan wasan da kocin Atletico Madrid ya yi, ya nuna cewa yana da matukar amfani a kungiyar.

Thomas kwararren dan wasan tsakiya ne da yake jan ragamar tsakiyar kungiyar musamman bayan sayar da Rodri ga Manchester City a kakar bara.

A gida kuma ya lashe  kyautar Gwarzon Dan Wasan Ghana sau biyu kuma magoya bayan kasar na ganinsa a matsayin Zidane.

Sannan kungiyoyi da dama irinsu Juventus da Liverpool da Manchester United duk sun yi zawarcin sa kafin ya zabi tafiya Arsenal.

Dan wasan mai shekara yana 26 na da kwarewa a abubuwa da dama da ake bukata wajen dan wasan tsakiya.

Don haka, Aminiya ta rairayo wasu abubuwa muhimmai da za su sa Partey ya sauya yanayin wasan Arsenal ta sayo shi a kan zunzurutun kudi har Fam miliyan 45 a lokacin annobar coronavirus da wasu kungiyoyi ba sa iya biyan cikakken albashi.

  • Yana ganiyarsa yanzu

A shekara 26, yanzu ne yake ganiyar kwallonsa domin ya samu duk wani horo ko kwarewa da ake bukata. Yanzu kawai sai baje kolin iyawa.

Yana da kwarewar buga tsakiya da ake kira box to box, wato dan wasan tsakiya da ke iya kula tare da kare ’yan wasan baya, da kuma kwarewa wajen hada tskanin ’yan wasan bayan da na gaba ta hanyar karbo kwallo daga baya, ya tura gaba.

Arsenal ta dade tana neman dan wasan tsakiya mai ganiya da karewa a tsakiya kasancewar wani lokacin takan yi amfani da dan wasan baya David Luiz a matsayin.

  • Shi ne na biyu wajen raba kwallo (Passes) a kakar bara a Atletco Madrid:

A kakar bara, Thomas Partey ne dan wasa na biyu wajen raba kwallo a kungiyar Atletico Madrid, inda ya samu kashi 41.2 da kuma dacewa wajen kai wa ga wanda ya aika, inda ya samu kashi 83 wajen dacewa.

Shi ne kuma dan wasa na uku wajen jefa kwallo daga nesa a gasar baki daya.

Wannan ya sa kungiyoyi da dama suke rububin sa ba ma Arsenal ba kadai.

Duk ’yan wasan tsakiyan Arsenal a kakar bara, babu wanda ya kai wannan nasarar.

Dani Cabellos ya samu nasarar raba kwallo da kashi 48, Granit Xhaka kashi 49, Matteo Guendouzi kashi 54, sai Lucas Torreira kashi 54.

Sannan yakan rike kwallo, inda a kakar bara aka kiyasta yana zaran akalla mutum biyu a duk wasa.

  • Kwarewa wajen kwato kwallo:

A kakar bara ya kwato kashi 63 na kwallon da ya bi a wajen abokan hamayya, wanda hakan kadai abin a yaba ne.

Shi ne kuma na hudu a gasar La liga wajen kokarin kwace kwallo a kafar abokan hamayya a kakar bara.

Bayan haka shi ne na hudu wajen tare kwallon da ake jafa mai nisa da aka jefo zuwa gidansu.

Ya samu katin gargadi guda 10, wanda ke nufin ba ya tsoron jefa kafarsa, matukar zai hana kwallo wucewa zuwa ’yan wasan bayansa.

  • Yana taimakawa ’yan wasan gaba

Karbo kwallo da yake yi ya tura gaba da kuma yadda yake kan gaba wajen jefa kwallaye daga nesa, na taimaka wa ’yan wasan gaba.

Arsenal na da fitattun ’yan wasan gaba, irinsu Pierre-Emerick Aubameyang da Willian da Alexandre Lacazette.

Akwai kuma irinsu Nicolas Pépé da sauransu da suka kware wajen zura kwallo, amma a lokuta da dama suke wahalar samun kwallaye daga tsakiya.

  • Me zuwansa a Arsenal ke nufi ?

Kasancewar Arsenal ta yi fice wajen iya raba kwallo, Thomas Partey zai kara samun damar raba kwallo yadda yake so.

Sannan ’yan wasan gabanta, wadanda babu shakka a kan kwarewarsu, za su rika samun kwallaye saboda ya kware wajen jefa kwallo daga nesa.

Duba da kwarewarsa a kusan duk abubuwa da ake bukata wajen dan wasan tsakiya, Partey dan wasa ne da kowane mai horar da ’yan wasa, ko kungiya ke bukata.

Bisa yanayin wasan Arsenal, kungiyar ta fi yin fice ne wajen takawa da raba leda.

Sai dai daga kakanni biyu da suka gabata bayan ta samu kwararrun ’yan wasan gaba, sai ya kasancewa kowace kungiya na tsoron ta.

Duk da haka ’yan wasan gaban kan sha wahalar gaske wajen samun isassun kwallayen da zu zura a ragar abokan hamayya.

Da yake bayyana babbar matsalar Arsenal, tsohon dan wasan kungiyar, Sol Campbell ya ce kungiyar na bukatar kwararren dan wasan tsakiya da zai lura da bukatun ’yan wasan gaba, sannan ya kare ’yan wasan baya.

A cewar Campbell, “babbar matsalar tana tsakiya ne. Ana matukar bukar wanda ya fahimci harkar sosai. Matsalar Arsenal yanzu a tsakiya kawai take.

“Za ka iya samun ’yan wasan baya da ’yan wasan gaba masu kyau, amma idan ba ka da kwararren dan wasan tsakiya da zai hada tsakani, to akwai matsala”, inji shi.

Zuwan Thomas Partey zai kawo wa Arsenal abubuwa da dama: ’Yan wasan baya za su samu sauki, sannan ’yan wasan gaba za su huta da zuwa neman kwallo.