✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda tirela ta kashe yara ’yan makaranta 15 a Legas

Ana fargabar akalla kananan yara 15 ne suka rasu, wasu da dama kuma sun samu ranunka

Yara ’yan makaranta akalla 15 ne ake fargabar sun rasu, wasu da dama kuma suka jikkata bayan wata tirela ta kwace ta auka musu bayan sun taso daga makaranta.

An shiga rudani a yankin Ojodu-Berger da ke Jihar Legas a ranar Talata, bayan kwacewar tirelar da irin asarar da ta janyo.

Wata majiya ta bayyana cewa akalla yara 15 sun mutu, sai dai ya zuwa lokacin hada wannan labari babu wani cikakken bayani a hukumance kan adadin wadanda suka rasu.

Lamarin ya rutsa da yaran ne a wurin da ’yan makarantar ‘Grammar School’ ke jiran mota idan an tashi daga makaranta.

Majiyar ta kara da cewa tirelar ta kwace wa direban ne sannan ya afka kan daliban da ke jiran mota a madakatar mota.

“Daliban makarantar sun fusata sannan suka cinna wa tirelar wuta. Wasu daga cikin daliban makarantar sun ji rauni sannan an garzaya da su asibiti,” a cewar majiyar.

Lamarin ya jawo cunkoson ababen hawa, wanda hakan ya sa ’yan kasuwa da ke gudanar da harkokinsu a yankin rufe shagunansu don gudun farmaki daga bata-gari.