✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda tsadar abinci ke sa satar garin tuwo a Kano

Halin matsi da tsadar kayan abinci sun sa wadansu mutane sun fara satar garin tuwo a wurin nika

Matsin tattalin arziki da tsadar kayan abinci sun sa wadansu mutane sun fara satar garin tuwo a injinan nika a Jihar Kano.

Unguwar Gobirawa Dukawa na daya daga cikin unguwannin da wannan ta’asa ta yi kamari.

Satar ta fara yawa – Masu nika

Aminiya ta tattauna da wani mai injin nika mai suna Malam Aminu Dukawa inda ya ce satar gari ta yi yawan gaske inda take tilasta wa mutane sa idanunsu a kan nikar da suke kawowa.

Malam Aminu ya ce, “Na kai shekara 20 ina wannan sana’a. A da wadansu za su kawo nika su mance da shi sai gari ya kai mako a jiye ba tare da an kula da shi ba.

“Amma a yanzu ba dama mutum ya ajiye gari sai a dauke masa, abin da muke fama da shi ke nan.”

Shi ma wani mai nika mai suna Malam Jamilu Adamu da ke Unguwar Barhana ya ce satar garin ta shafi rumfarsu inda a mako guda aka sace garin sama da mutum 10.

“Kowa ya san yadda ake nikan gari a irin wadannan rumfuna namu, yawanci mutum kan kawo ya ajiye sai wani lokaci ya zo ya dauka.

“Abin da ke faruwa shi ne saboda an saba da haka sai ya janyo wadansu suna amfani da wannan dama su zo su dauki garin da ba su suka kawo nika ba.

“Mu kuma a namu bangaren saboda abin da yawa ba kowa ne mai nika ya sani ba.

“Da mutum ya zo ya nuna maka garinsa sai kawai ya dauka ka fada masa kudin nika ya biya ya yi tafiyarsa.

“A nan rumfar an sace wa mutane da dama garinsu ba tare da saninmu ba”, inji shi.

‘Yadda na dauki mataki’

A ziyarar da Aminiya ta kai Unguwar Dandinshe Gabas ta tattauna da Malam Hassan Mainika wanda ya ce an fara satar gari a shagonsa ne kwanakin baya amma ya yi gaggawar daukar mataki a kan lamarin.

“Gaskiya ni ba a dade ana satar gari a shagona ba, domin ana satar gari sau daya zuwa biyu na yi maganin abin.

“Sai na sanya doka duk wanda ya kawo nika dole ya tsaya ya dauki kayansa idan ba haka duk abin da ya faru babu ruwana.

“Domin na san ba za mu iya kiyaye dukkan garin da ake kawo mana nika a wannan wuri ba”, inji shi.

Masu nika na asara wajen biyan masu gari

Binciken Aminiya ya gano cewa al’amarin satar garin tuwon ya jefa masu nika a cikin wani hali saboda yadda suke biyan garin da aka sace a shagunansu.

Malam Aminu ya ce ya biya kimanin Naira dubu 10 na kudin garin da aka sace a lokuta daban-daban.

“Akwai lokacin da wani ya kawo nikan masara da ya zo dauka sai aka nemi garin aka rasa.

“Mu kuma mun tabbatar ya kawo nikan don kowa ya ga lokacin da ya ajiye.

“Don haka ya ce ba zai yarda ba dole sai an biya shi masararsa wacce ta kai kwano 10, haka muka biya shi.

“Ban da kuma wadansu masu kwano dai-dai zuwa bibbiyu da hakan ta faru da su muka biya a lokuta daban -daban.”

Masu nika sun fara daukar mataki

A yanzu haka yawancin masu sana’ar nikan garin sun dauki matakin buga katin shaida da suke bayar da shi ga duk wanda ya kawo nika.

A cewar Malam Jamilu, “Mun ga abin ya yi yawa kuma duk inda aka je aka dawo abin kanmu yake karewa don haka muka dauki mataki.

“A yanzu mun buga katin shaida da ke dauke da lambobi a jiki.

“Idan mutum ya kawo nikansa sai mu daye wata takardar daga jikin katin mu manna a jikin buhu ko kwaryar da ya kawo nikan.

“Sannan mu ba shi katin ya tafi da shi. Idan mutum ya zo ba katin ba za mu ba shi garin ba ko da kuwa mun san nasa ne,” inji shi.

Yadda aka sace mana gari

Aminiya ta tattauna da wadansu da aka sace wa gari a injinan nika, inda suka ce sun dauki matakin tsayawa a nika musu hatsinsu maimakon a baya da suke bari sai wani lokaci su dawo su dauka.

Malam Rabi’u Barhana ya ce duk da tsawon lokaci da ake dauka kafin layi ya zo kansa ya gwammace ya jira don kada garinsa ya yi batar dabo.

“Duk da cewa babu dadi mutum ya yi ta jira layi ya zo kansa, amma a yanzu tsayawa nake yi in kasa in tsare har sai an nika min hatsina sannan in tafi gida.

“Na daina ajiye nika in je na dawo saboda an yi sha ni na warke. Akwai ranar da na kawo nika da na dawo dauka sai na tarar an sace, don haka na dauki wannan mataki,” inji shi.

Wani yaro da Aminiya ta iske yana jira a nika masa hatsi mai suna Salisu Ahmad ya ce sakamakon satar garin da ake yi, ya sa yake jira a nika masa sannan ya tafi da shi gida “Kasancewar an taba sace mana gari a nan ya sa mahaifiyata ta ce in tsaya in tafi da garin gudun kada a sace mana,” inji shi.

Dukkan mutanen da Aminiya ta tattauna da su sun danganta satar garin da halin da ake ciki na tsadar kayan abinci da talauci.

“Babu abin da ya jawo haka illa talauci da yunwa da mutane ke ciki.

“Wallahi mutane suna cikin wani hali. Don Allah gwamnati ta tallafa wa mutane don fitar da su daga halin kuncin da suke ciki,” inji su.