✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni 31 da suka taba zama, ko suke son zama Sanatoci a Najeriya 

Ga jerin Gwamnoni masu ci da tsofaffi da ke son zama Sanatoci

Wani abin da ya zama kamar al’ada bayan kowanne babban zabe a Najeriya shi ne komawar Gwamnonin da wa’adinsu na mulki ya kare zuwa Majalisar Dattijai a matsayin Sanatoci.

A cewar wasu jama’a, Majalisar ta dauko hanyar zama matattarar tsofaffin Gwamnonin da za su dawwamar wa kansu kudaden alawus da na fansho ribi biyu.

Wasu kuma na ganin cewa hakan ba zai ba su damar samar wa da talaka dokokin da suka shafe shi ba. Saboda kare muradunsu kawai su ke yi.

Tuni dai wasu kungiyoyi ke ta kiraye-kirayen dakatar da wannan kaka-gidan da gwamnonin ke yi a majalisar domin ba wasu dama su ba da ta su gudunmawar ta gina kasa.

Aminiya ta yi nazarin jerin sunayen tsofaffin Gwamnonin da a yanzu suke a majalisar dattijai da Jihohin da suka fito;

  1. Kalu Orji               –    Abiya
  2. Gabriel Suswan     –   Binuwai
  3. Kashim Shetima     –   Borno
  4. Samuel Egwu        –    Ebonyi
  5. Nnamani Chimaroke   –   Enugu
  6. Danjuma Goje         –     Gombe
  7. Ibrahim Shekarau     –    Kano
  8. Kabiru Ibrahim Gaya   –   Kano
  9. Adamu Alliero      –     Kebbi
  10. Ibukunle Amosun     –    Ogun
  11. Aliyu Wammako      –   Sakkwato
  12. Ibrahim Geidam      –     Yobe
  13. Rochas Okorocha    –     Imo

Ga kuma jerin sunayen Gwamnoni  masu ci da suke zawarcin kujerar Sanatocin da zaran wa’adinsu na nulkin ya kare.

  1. Okezie Ikpeazu       –      Abiya
  2. Ifeanyi Ugwuanyi     –    Enugu
  3. Dairus Ishaku       –     Taraba
  4. Gbenga Daniel       –      Ogun
  5. Abubakar Sani Bello     –   Neja
  6. Simon Lalong      –    Filato
  7. Samuel Ortom     –      Binuwai
  8. Dave Umahi       –      Ebonyi
  9. Aminu Tambuwal     –   Sakkwato
  10. Atiku Bagudu        –      Kebbi

Wannan kuma jerin sunayen wasu tsofaffin Gwamnonin da su ka yi Gwamnoni a da, da kuma Jihohin da suka fito.

  1. Umar Tanko Almakura   –   Nassarawa
  2. Saminu Turaki      –     Jigawa
  3. Adams Oshiomhole     –     Edo
  4. Ibrahim Dankwambo    –   Gombe
  5. Ali Modu Sheriff           –  Borno
  6. Rabiu Musa Kwankwaso    –     Kano
  7. Abdullahi Adamu    –     Nasarawa
  8. Ahmed Makarfi       –      Kaduna