NAJERIYA A YAU: Laifin Wane Ne Rashin Daukar Masu Digiri Aiki a Najeriya? | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Laifin Wane Ne Rashin Daukar Masu Digiri Aiki a Najeriya?

    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao da Bilkisu Ahmed

Domin sauke shirin latsa nan

Rashin samun aikin yi a tsakanin wadanda suka kammala karatu mai zurfi na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya, har wasunsu na yin da-na-sanin bata shekarunsu a yin karatun.

Masana kuma na dora laifin rashin aikin yi a tsakanin matasa masu ilimin boko a kan rashin ingancin manhajar karatun kasar. Shin a ina gizo ke saka?

Shirin Najeriya A Yau na tafe amsar wannan tambaya.