✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda uwargida za ta adana naman Layya

Ga wasu hanyoyi da za ku adana namanku na Sallah domin ya jima kuna amfana da shi.

A lokacin Babbar Sallah ko Sallar Layya nama na wadatuwa, sai dai  kuna yawan cin shi yakan haifar da illa.

A dalilin haka ne mutane da dama suke neman hanyoyin da za su adana naman Sallah dinsu yadda zai jima suna ci.

Ga wasu hanyoyi da za ku adana namanku na Sallah domin ya jima kuna ba tare da ya lalace ba.

Danyen nama

Babbar hanya ko hanya mafi sauki ta adana danyen nama ita ce sanya shi a firinji wanda yake kasancewar a cikin sanyi koyaushe.

Sanyi yana hana kayayyaki lalacewa ba wai kawai sai nama ba.

Wata hanyar ita ce ta shanya danyen naman bayan an yayyanka shi da fadi kamar za a yi kilishi da shi.

Sai a sa gishiri a barbade naman da shi a shanya a igiya ya bushe.

Amma a sani cewa wannan hanya tana da hadari ga lafiyar dan Adam saboda irin kudaje da ke bin naman wajen shanya.

Don haka sai an kula sosai wajen girka shi don guje wa abin da ka je ya zo.

Naman kai ko ganda

Idan aka sami fatar saniya akan shanya ta yadda za ta bushe sannan a ajiye a rika diba ana amfani da ita lokacin da ake bukata.

Shi kuma naman kai ana iya ajiye shi bayan an farfasa shi kanana, sai a barbada masa gishiri a soya shi cikin mai sama-sama sannan a shanya shi.

Amma fa dole sai an dinga kula da yadda shanyarsa take domin idan ya dade a ajiye ba tare da juya shi ba to zai iya lalacewa ya yi tsutsa.

Danbun nama

Babbar hanyar da ke hana dafaffen nama lalacewa shi ne ta hanyar sarrafa shi ya zama danbu.

Idan nama yana matsayin dambu to babu abin da yake bukata wajen adanawa matukar dai ya soyu sosai.

Idan uwargida ta dafa naman sosai ya yi laushi sai a daka shi a turmi sannan a juye shi a babban faranti domin ya sha iska sannan a sa mai sosai a wuta a fara soyawa.

Amma ba a sa masa wuta sosai don kada ya kone.

Idan ya soyu sai a zuba shi a mataci don man ya dige.

Za a iya barin shi a haka har zuwa washegari sannan sai a juye shi a mazubi.

Soyayyen nama

Yana da kyau tunda farko idan uwargida ta tashi soya naman to ta tabbata ta bar shi ya soyu sosai ya yi duhu, amma fa ba wai a bar shi ya kone ba.

Don haka ba wuta ake babbaka masa ba.

Idan ya soyu za a ga cikinsa ya yi jawur, sai a kwashe shi a zuba a mataci don naman ya tsane.

Idan ya tsane sai a kwashe shi daya bayan daya a zuba a faranti domin idan aka juye shi diddigar naman za ta iya sa shi ya lace cikin sauri.

Sai a bar shi ya huce sosai kamar misalin ya kwana a shanye.

To shi nama ko soya shi aka yi idan ba a dauki matakai ba na adana shi lalacewa yakeyi ya rube.

Za a iya adana shi afirinji kamar yadda kowa ya san cewa sanyi na hana abubuwan amfani musamman ma abinci lalacewa ba kawai ya ta’allaka a nama ba.

Yadda ake yi shi ne a samu firinji wanda ake yawan kunna shi a zuba naman bayan an soya shi, sai a sa ya yi sanyi, lokacin da ake bukata saia a dauko a dumama.

Akwai kuma wata hanyar ta barbada wa soyayyen naman gishiri sai a bar shi ya sha iska sosai.

Idan ana son a yi amfani da naman bayan wani lokaci sai a dauko shi a wanke naman sosai wato a wanke duk gishirin sai a sulala shi a saman tukunya a ci.

Ana kuma iya ajiye mama a cikin man da aka yi suyar naman da shi.

Ko shakka babu da an samu irin wannan man sai a zuba nama a cikin shi amma a sani sai an bar duka naman da man sun yi sanyi sosai sannan a zuba a ciki.

Sannan a tabbatar cewa man ya rufe dukkan naman.

Wannan ma wata hanya ce wacce ake ajiye naman; Ida an tashi sai dai kawai a dauko a sulala shi.

Duka wadannan hanyoyi da muka ambata idan an ajiye naman a tabbatar ana duba shi koda za a ga wani canji, sai a dauki matakin gyara don kada ya lalace.