✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wahalar mai ta jefa Jasawa cikin halin ni-’ya-su

Wakilinmu ya ga yadda akasarin gidajen mai a birnin suka kasance a rufe.

A yayin da ’yan Najeriya ke fuskantar wahalhalu a sanadiyyar karancin man fetur da ake fama da shi a ’yan kwanakin nan, mazauna Jos a Jihar Filato sun ce yanayin ya jefa su cikin halin ni-’ya-su.

A zagayen da wakilimu ya yi a garin na Jos, babban birnin Jihar,ya gane wa idanunsa yadda mazauna garin suka shiga cikin mawuyacin hali sakamakon karancin man.

Wakilinmu ya ga yadda wasu gidajen mai a birnin suka kasance a rufe yayin da gidajen da suka bude kum suke sayar da lita daya a tsakanin N185 zuwa N200.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amarin, tsohon Shugaban Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW) reshen tashar mota ta Bauci Eoad da ke Jos, Alhaji Habibu Abubakar ya ce yanzu Jasawa na cikin mawuyacin hali kan wannan matsala ta rashin mai.

Ya ce, “Gwamnati ce ta kawo wannan matsala, saboda ta yi barazanar kara kudin mai amma jama’a suka ki yarda.

“Don haka ta rike mai don a shiga wahala, idan mutate suka shiga wahala, sai su ce garama a kara. Dama haka ake yi a Najeriya, sama da shekara 30.”

Shi na wani direban babur mai kafa uku, Yakubu Idris ya ce, suna fuskantar kalubale na rashin man, wajen gudanar da aikinsu.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin masu gidajen mai da ’yan bunburutu kan wannan lamarin, amma sun ki yarda su tattauna da shi.