✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dattijo ya yi auren fari bayan shekara 74

Da a ce Allah bai tsara hakan ba, da kila har yanzu ban yi auren ba.

Wani mazaunin unguwar Up Garage da ke birnin Lokoja a Jihar Kogi, Mallam Muhammad Awwal, ya cika babban burinsa bayan ya yi auren fari yana da shekaru 74 a duniya.

Awwal wanda shi kadai ne namiji a cikin yaya biyar da iyayensa suka haifa, ya auri amarya mai shekara 45, Rahmat Muhammad watanni shida bayan rabuwarta da tsohon mijinta.

Aminiya ta ruwaito cewa, an daura auren Mallam Awwal da amaryarsa a ranar Lahadin da ta gabata a bisa koyarwar addinin Islama.

Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin Awwal dai tamkar wanda aka yi wa asiri da ya rika ganin samu yana ganin rashi.

’Yan uwansa sun ce duk lokacin da maganar aurensa ta tashi sai ta mutu ba tare da an je ko’ina ba a duk tsawon wannan shekaru.

“Duk lokacin da ya fara neman aure, sai maganar ta kusan tabbata sai kuma ta watse.

“Ya kasance yana fama da wannan kaddara har sai a yanzu da Allah Ya amsa addu’arsa,” in ji wani dan uwansa da ya bukaci a sakaya sunansa.

Mallam Awwal wanda yake sana’ar wanki da gudu tsawon shekaru 49 da suka gabata, an yi masa kyakkyawar shaida ta gaskiya da rikon amana da kuma kwarewa a kan sana’arsa.

Rahotanni sun ce Mallam Awwal ya fito ne daga gidan mutunci wanda Kawu ne ga wani sanannen lauya a garin Okene, Barista Abdullahi Aliyu.

Taron daurin auren Mallam Awwal ya samu halartar dimbin mutane saboda yadda ya jima ba tare da ya yi aure ba.

Mutane da dama da suka halarci daurin auren sun nuna masa kauna, inda suka yi tururuwar halarta ba tare da la’akari da mamakon ruwan sama da ke sauka ba a safiyar da aka daura auren.

Na kusa na fitar da rai zan yi aure —Mallam Awwal

Da yake jawabi fuskarsa cike da annuri, Mallam Awwal ya ce saura kiris ya fidda rai zai yi aure har sai da Allah Ya hada shi da matarsa Malama Rahmat.

Mallam Awwal wanda ya bayyana talauci a matsayin babban dalilin da ya hana shi aure tsawon wadannan shekaru, ya ce an sha ba shi shawara da kwarin gwiwa a kan ya yi aure amma yana watsi da hakan.

“A koyaushe ina fargabar na gaza sauke nauyin iyalina idan na yi aure, domin kuwa aure ba abun wasa ba ne.

“Duk don saboda haka na rika gudun aure, amma a yanzu Allah Ya sa hakan ya tabbata,” inji shi.

Ya bayyana cewa, mata da yawa sun yi watsi da tayin soyayyarsa a lokutan baya musamman lokacin da yake matashi.

Ya ce, “lokacin da nake matashi, mata da yawa sun rika min kallon hadarin kaji saboda ba ni da abun hannu, amma a yanzu ina godiya ga Allah saboda duk wannan ya zama tarihi.”

Ya kara da cewa, “da a ce Allah bai tsara hakan ba, da kila har yanzu ban yi auren ba duk da a yanzu ina da rufin asiri.

Ya yaba wa matarsa, yana mai cewa, “bayan kasancewarta kyakkyawa, tana kuma da kankan da kai da fahimta da kuma riko da addini doriya a kan sanin duk wasu rukunai na aure.

“Allah ne kadai Ya sani ko za mu samu haihuwa don babu wanda ya san abin da Allah zai Yi saboda komai a hannunSa yake”

Matarsa ta ce kaddara ce ta hada su suka zama mata da miji, kuma tana addu’a Allah Ya cika musu burinsu tare.