✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wasan Man City da Real Madrid zai kasance

Idan Manchester City ta doke Real Madrid a wasan, to kocinta, Pep Guadiola, ya zama wanda ya fitar da Madrid sau uku a Gasar Zakarun…

A daren ranar Laraba za a fafata wasan gab da kusa da na karshe na Gasar Zakarun Turai tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa guda biyu wato Manchester City da Real Madrid wanda ma’abota kallon kwallon kafa suke ganin shi ne wasa mafi zafi a bana.

Idan Manchester City ta doke Real Madrid a wasan, to kocinta, Pep Guadiola, ya zama wanda ya fitar da Madrid sau uku a tarihin Gasar Zakarun Turai.

A baya dai kungiyoyin sun taba haduwa har sau shida a wasannin Zakarun Turai, inda kowace kungiya ta yi nasarar cin wasa biyu-biyu a tsakaninsu, sannan a sauran wasannin biyu aka yi kunnen doki.

Wannan shi ne karo na bakwai da kungigoyin ke haduwa a gasar cin kofin Zakarun nahiyar Turai.

Na baya-bayan nan dai shi ne na shekara ta 2019/20 inda Man City ta ci Madrid gida da waje — 1-2 a gidan Madrid sai kuma 2-1 a gidan Man City, wanda hakan ya ba wa Man City damar kaiwa gurbin gab da na kusa da na karshe.

Real Madrid

Sai dai Real Madrid ita ce kungiyar da ta fi kowacce kafa tarihi a wannan gasa a duniya, inda ta lashe har sau 14.

Irin namiji kokarin da kungiyar ke yi a baya-bayan nan, musamman ma dan wasan gananta, Karim Benzema, wanda ya ci kwallo bakwai a wasanni uku da kungiyar ta buga a gasar, tare da kwallo uku-uku har sau biyu a wasansu da PSG da kuma Chelsea.

Hakazalika a yanzu kungiyar ta ci dukan wasanninta a jere da ta buga ba a gida ba, inda ta zura kwallo akalla uku a dukkan wasannin da ta buga din.

Wannan ya sa magoya bayan kungiyar ke ganin cewa lallai kungiyar Man City za ta kwashi kashinta a hannu a wasansu da Madrid, wanda za a buga a filin wasa na Etihad da misalin karfe 8 na dare.

Manchester City

A bangare guda kuma Man City rabon da a yi nasara a kanta a gidanta tun 2018 da Lyon ta ci su da ci 2-1 — wato yanzu kimanin shekara 4 ba a yi nasara a kanta ba a Etihad.

Hakazalika ta zura kwallo har 13 a raga a cikin wasanninta biyar a Gasar Zakarun Turai da ta buga a gida, inda a wasanninta biyu na karshe ba a zura musu kwallo ko daya ba a ragarsu.

City dai ta ci wasanninta uku cikin shida tare da yin kunnen doki sau biyu a wasanninta da ta buga.

A satin da ya gabata dai kungiyar ta Manchester City ta lallasa Watford 5-1 a Gasar Firimiyar Ingila.

Hasahsen yadda za ta kaya

Magoya baya da sauran masu adawar Madrid suna ganin cewa ko a bana tarihi zai iya maimaita kansa a tsakanin kungiyoyin biyu, inda suke tunanin City ce za ta yi nasarar fitar da Madrid kamar yadda ta yi a haduwarsu ta baya.

A tarihi dai babu wani mai horas da ’yan wasa a duniya da ya samu nasara a kan kungiyar Madrid da yawa kamar kochin Manchester City wato Pep Guardiola.

Idan dai har kungiyarsa ta yi nasarar fitar da Madrid a wannan wasan ta gab da karshe, to ya zama kocin da ya fitar da Madrid har sau uku a Gasar Zakarun Turai.

Sai dai idan za a iya tunawa a haduwar karshe da wadannan masu horaswa suka yi  a Gasar Zakarun Turai, Carlos Ancelotti, ne ya yi nasara a kan Pep Guardiola, a lokacin da Real Madrid ta lallasa Bayern Munich ci 5-1 a gida da waje, wanda hakan ya kai  Madrid zagaye na karshe tare kuma da lashe gasar a shekara ta 2014.