✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wasan mota ke jefa rayuwar matasa cikin hadari

Duk da hadarin da ke tattare da wasan mota, har yanzu matasan ba su daddara ba.

Matasa daga wurare daban-daban kan taru a duk ranar Lahadi domin nuna irin kwarewarsu a tuki da wasan mota a birnin Abuja.

Wadannan masu wasan mota kan hallara a wuraren ne a cikin motoci na alfarma iri-iri su yi ta kwabo da su cikin nishadi da farin ciki, ’yan kallo kuma suna jinjina musu, abin sai wanda ya gani.

A wasu lokuta, masu wasan motar kan yi raye-raye da bushe-bushe, duk da cewa a wasu lokutan wasan kan jawo afkuwar hadurra.

Duk da cewa a yayin wannan wasan akan samu matsala, har yanzu matasan ba su daddara da irin hadarin da yake yawan jefa rayuwarsu a ciki ba.

Alal misali, mota kan kwace wa matukinta, a yayin da yake tsaka wasa da ita ta yi hatsari.

Idan irin hakan ko makamancinsa ya taso, su kansu ’yan kallo ba su tsira ba, saboda ba kowane mai wasa da mota da ya shiga wasan ba ne kwarare.

Wasu ba su ma gama koyon tukin ba, amma saboda rawar kai da rashin hangen nesa da ganganci irin na matasa, sai ka ga sun shiga sun yi kane-kane, saboda jin ana jinjina wa masu wasan.

Amma ko da wani hadari ya auku, wannan ba zai hana a ci gaba ba da wasa ba, sai dai wanda ta shafa ya koma gefe ko a komar da shi, a dora daga inda aka tsaya — idan ta baci sosai kuma a bari sai wani makon.

A ranar Lahadi, 19 ga watan Disamba, 2021, a Abuja, ana tsaka da wasan a filin ajiye motoci da ke Ma’aikatar Shari’a, sai masu shiryawa suka yanke shawarar a koma wani waje.

Cikin dan kankanin lokaci ’yan kallo da masu wasa suka dunguma suka kama hanya zuwa sabon wurin, sai gudu suke da motoci a hanyar kwaryar birnin Abuja, Central Area.

Ana cikin haka ne wani matashi daga cikinsu da ke dauke da wasu ’yan mata a cikin motarsa ya daki bayan wata motar dake gabansa.

Hadarin ya kassance mai muni, domin kan ka ce kwabo, gaban motarsa ya yi kaca-kaca, ba kyan gani.

Amma dai Allah Ya kiyaye babu wanda ya ji rauni a cikin mutanen da ke cikin motar.

Bacin hadarin da ke tattare da masu wasan mota, akwai matsalar da ta shafi masu zuwa kallo.

Mutane kan taru a irin wadannan wurare ne kawai, babu wani tantancewa, kuma a waje irin wannan, ba ka raba su da bata-gari da masu laifi.

Shaye-shaye a baina jama’a kadan ne daga cikin matsalolin da ake gani na zahiri a tattare da taruwar jama’a a irin wadannan wurare.

A wannan yanayi na rashin tsaro da kasar nan take ciki kuma, ya kamata masu shirya irin wadannan wassani su rika tuntubi jami’an tsaro, ko domin a tabbatar da amincin jama’a.

Su kansu masu wasan, ya kamata su rika amfani da kayan kariyar kansu da na motocin, ko da wani abu zai faru.