✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda WhatsApp ya kwace mu daga ’yan bindiga —Daliban Kaduna

Ba don jami'an tsaro sun kawo dauki ba, da watakila 'yan bindigar sun tafi da kowa.

Wani dalibin Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke, Afaka, Jihar Kaduna ya ce tattaunawar da suke yi a shafin sadar da zumunta na WhatsApp da suke yi a marakanta ne ya yi silar tura jami’in tsaro da suka kubutar da su a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari.

Ateb Daniel, da ke shekararsa ta karshe a sashen Fasahar Kirki a Kwalejin ya shaida wa Aminiya cewa: “Ina ganin da babu kafafen sada zumunta, da sun samu (’yan bindigar) sun samu sauki, saboda babu wanda ke da tunanin yin kira; tura sako ne abu mai sauki kuma wanda a zahiri ya cece mu a halin da ake ciki.”

“Muna da dandalin sada zumunta wanda a nan tattaunawa ta makaranta kuma a nan ne muka fara sanya cewa akwai matsala a cikin makarantar kuma shugabannin makarantar suka sanar da hukuma,” inji shi.

Daniel wanda har ilayau shugaba ne na kungiyar dalibai ya ce ‘yan bindigan sun shirya tsaf domin gudanar da aikin inda ya kara da cewa mafi yawan daliban sun tsere cikin daji yayin harin.

“Dukanmu mun gudu mun buya a cikin daji don haka lokacin da sojoji suka zo, wasu abokanmu ke kiran mu sannan a zo su dauke mu a wuraren da muka buya.

“An yi dauki ba dadi da ‘yan fashin saboda sun shirya tsaf don aikin. Ba don taimakon jami’an tsaro ba, ina ganin da sun tafi da duk wanda ke makarantar gaba daya,” inji shi.