✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wutar lantarki ta kashe mai fenti da yaransa 5

Mazauna garuruwan Saminaka da Sigau a Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, sun hadu da tashin hankali a yammacin ranar Asabar da ta gabata.…

Mazauna garuruwan Saminaka da Sigau a Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, sun hadu da tashin hankali a yammacin ranar Asabar da ta gabata.

A yankin ne wutar lantarki ta kone wani mai aikin fenti da ke zaune a Saminaka; Malam Aminu da babban dansa, Masa’udu Aminu da kuma yaran aikinsa 4: Babawo Kyauta da Auwalu Musa da Bashiru Munka’ila da kuma Safiyanu Sigau da suke zaune a garin Sigau.

Da yake yi wa wakilinmu bayani kan yadda lamarin ya faru, daya daga cikin ’ya’yan marigayi Aminu Maifenti, mai suna Abubakar Aminu ya ce kamar yadda labari ya zo musu, daga

wani da al’amari ya faru a gabansa, ya ce suna zaune da babansu zai yi alwala ya yi Sallar La’asar, sai ya ce in Allah Ya yarda, za su gama aikin fentin a ranar, saboda washegari zai tafi Ilori, akwai aikin fenti da zai yi a can.

Ya ce ya fara alwalar, sai ya ce yaran su kama karfen da ake hawa idan ana aiki, wato sikafur su matsa da shi, idan suka idar da Sallah, sai su karasa aikin.

Abubakar ya ce an shaida musu cewa da yin wannan magana ko minti biyu ba ayi ba, bayan ya yi alwalar yana tashi sai ya kira su yaransa, suka kama karfen suna turawa inda za su karasa aikin, sai karfen ya taba babbar wayar layin wutar lantarki ta garin da ke kusa da wajen.

Ya ce mai ba su labarin ya ce yana juyawa, sai ya ga duk sun kandare a jikin karfen, suna ci da wuta.

Haka suka rika nadewa a jikin karfen, kamar leda suka yi baqi, wadansu har kayan cikinsu ya fito. Ana ji ana gani, babu yadda za a yi, har suka rasu.

Abubakar Aminu ya ce a tsawon rayuwarsa, bai taba jin abin da ya firgita shi ba, kamar wannan lamari.

Domin sun rabu da mahaifinsa da safe, lafiya-lafiya lokacin da zai tafi aikin.

Ya ce mahaifiyarsu ta fere doyar za a dafa musu sai wannan mammunan labari ya zo musu.

Ya ce dukkan yaran aikin nasa da suka rasu, suna cikin wadanda ya shirya zai tafi da su Ilori, domin aikin da za su yi.

“Mahaifinmu yana zuwa aiki a wurare da dama da aka gina gidan mai na A. A. Rano, yana yi

musu aikin fenti, domin yana tare da daya daga cikin injiniyoyin da suke yi wa A. A. Rano aikin gina gidajen mai a kasar nan”, inji shi.

Ya ce mahaifinsu ya rasu ya bar ’ya’ya 17, kuma wadanda suka rasu tare da shi, mutum daya ne, bai yi aure ba amma sauran, kowa yana mata da ’ya’ya.