✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda yajin aikin NLC ya jefa Jihar Kaduna cikin duhu

Ma'aikatan wutar lantarki a Kaduna sun shiga yajin aikin NLC na kwana biyar.

Al’ummar Jihar Kaduna sun shafe kwana biyu cikin duhu bayan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na TCN da ke jihar ya duke wutar.

Tun da sanyin safiyar Lahadi kamfanin ya dauke wutar a fadin jihar, bayan da TCN ta datse layin wuta na 33kv.

Bayan kusan awa 48, da misalin karfe 10:30 na daren ranar Litinin kamfanin ya dan hasko wutar, amma murna ta koma ciki domin ba a yi minti 15 ba, ya sake dauke wutar.

Kawo yanzu babu wani cikakken bayani game da dawowar wutar da aka dauke saboda yajin aikin da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) take yi a Jihar ta Kaduna.

Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) reshen Jihar Kaduna, ta bi sahu a yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da NLC ta fara a ranar Lahadi, kan sallamar da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi wa ma’aikata kusan 11,000.

Shugaban Sashe Hulda da Jama’a na TCN a Jihar Kaduna, Abdulazeez Abdullahi, ya nemi afuwar mutanen jihar kan rashin wutar, ta wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.

Dalilin yajin aikin

Ana sa ran Gwamnatin Kaduna da Kungiyar Kwadago za su koma teburin sulhu don nemo mafita game da yajin aikin da suka tsunduma.

Gwamnatin Kaduna na shirin sallamar ma’akatanta kusan 11,000 inda za ta yi wa wadanda shekarunsu na haihuwa suka kai 50 ritaya na dole.

Za kuma ta yi wa ma’aikatan da matakinsu na aiki ya kai 14 zuwa sama ritaya dole, ko da shekarunsu na haihuwa ba su kai 50 ba.

Ta kuma kayyade yawan ma’aikatan da kowace Karamar Hukuma za ta dauka zuwa mutu 50.

Ma’aitan da matakinnu ya yi kasa da mataki na 7 kuma duk za ta mayar da su ma’aikatan wucin gadi.

NLC na zargin El-Rufai da gallaza wa ma’aikata ta hanyar bullo da dabarun takura da za su sa aiki ya fita a ransu.

Tana kuma zargin sa da rashin biyan hakkokin ’yan fansho ta hanyar fakewa da sunan tantancewa, da biyan ma’aikata da ke mataki na takwas kasa da alabshinsu da sauranu.

Tuni dai El-Rufai ya ce babu gudu babu ja da baya a matakin na sallamar ma’aiakata, yana mai cewa hakan ya zama wajibi saboda albashin ma’aikata ke cinye fiye da kashi 80% na kudaden da jihar take samu daga Gwamnatin Tarayya.