✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga ke neman hana shiga da fita a Kaduna

Ga dukkan alamu dai hare-haren ’yan bindiga da ke ci gaba da tsananta a sassa daban-daban na Jihar Kaduna na neman hana duk wani shige…

Ga dukkan alamu dai hare-haren ’yan bindiga da ke ci gaba da tsananta a sassa daban-daban na Jihar Kaduna na neman hana duk wani shige da fice a fadin jihar.

Wannan hange dai na da nasaba ne da yadda a bayan nan ’yan bindigar suka kai wasu hare-hare a fannonin sufuri uku da ake amfani da su ciki har da wanda ya auku a filin jirgin saman Kaduna da wanda suka kai kan wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.

A ranar Litinin din da ta gabata ce ’yan bindiga suka dasa wa wani jirgin kasa bam a kan layin dogo wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna makare da fasinjoji.

Aminiya ta gano cewa jirgin wanda ta taso daga tashar jiragen kasa ta Idu da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, ya taka bam din ne a garin Katari, kimanin mintina 30 kafin ya isa tashar Rigasa a Kaduna.

Sakamakon kazamin harin da ’yan bindiga suka kai ne a kan jirgin fasinjar da ke zirga zirga tsakanin Kaduna zuwa Abuja wanda ya yi sanadiyar kashe mutane 7 da kuma jikkata wasu da dama, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira taron shugabannin hafsoshin tsaro na gaggawa domin tattauna matsalar.

Rahotanni sun ce shugaban ya bayyana bacin ransa da lamarin wanda ya kai ga rasa rayuka, inda ya bukaci hafsoshin tsaron da su kara kaimi wajen murkushe ’yan bindigar da ke zafafa hare-harensu a wannan lokaci.

Buhari wanda ya bukaci kubutar da duk fasinjojin da aka sace da kuma tabbatar da ganin an hukunta wadanda suka aikata laifin, ya kuma bai wa hafsoshin tsaron umurnin harbe duk wanda aka gani yana dauke da bindiga kirar AK47 ba tare da izini ba.

Shugaban kasar ya ce ba za su lamunce yadda wasu ke hana jama’a zaman lafiya ba, kuma kamar kowanne dan Najeriya shi ma ya kadu da wannan hari wanda shi ne irinsa na biyu wanda ya kai ga rasa rayuka da kuma jin rauni.

Kafin dai gudanar da taron, shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahya ya garzaya Jihar Kaduna inda aka samu hadarin domin gane wa idonsa halin da ake ciki, inda ya umurci dakarunsa da su gaggauta kubutar da wadanda ’yan bindigar suka sace.

Wata fasinjar jirgin da ta tsallake rijiya da baya, ta bayyana wa manema labarai cewar zuwan jami’an soji da ’yan sanda ne ya kubutar da su daga hannun ’yan bindigar wadanda suka fara kwashe mutane suna kaiwa daji.

Wani fasinja kuwa ya tabbatar da mutuwar mutane 7 sakamakon harin, yayin da wasu da dama suka samu raunuka, cikin su har da tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Ibrahim Wakalla Muhammad.

Tuni shi ma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ziyarci birnin Kaduna domin ganewa idonsa halin da ake ciki da kuma ziyarar fasinjojin da suka samu raunuka sakamakon kazamin harin.

Wannan hari na zuwa ne kwana biyu bayan wanda ’yan bindigar suka kai kusa da tashar jiragen saman Kaduna, abinda ya kai ga hallaka 12 daga cikin su.

Kasa da sa’o’i 24 da harin da ’yan bindiga suka kai kan jirgin kasa ne kuma makamancinsa ya sake auku a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja wanda motoci da sauran ababen hawa suka saba bibiya kasancewarsa tamkar wata mahada tsakanin Kudanci da Arewacin kasar.

Rahotanni dai na cewa shi ma a wannan harin kamar yadda ta saba kasancewa, ’yan bindigar sun yi awon gaba da matafiya, inda wasu shaidun gani da ido suka ce sun hangi ’yan bindigar suna tisa keyar gomman mutane zuwa dokar daji.

Harin Filin Jirgin Sama

A Asabar din ta gabata ce ’yan bindiga suka harbe wani ma’aikacin filin jirgin saman Kaduna da ke aiki da Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya (NAMA) mai suna Shehu Na’Allah.

Na’Allah ya gamu da ajalinsa ne lokacin da maharan suka yi yunkurin shiga filin jirgin, bayan sun yi musayar wuta da jami’an tsaro a kusa da filin, kodayake ba su samu damar shiga ba.

Wannan lamarin dai ya tilasta aka soke tashin wani jirgi da ke shirin zuwa Legas daga filin.

Hakan ce kuma ta sanya Kamfanin Jiragen saman Azman ya sanar da dakatar da jigila a filin tashi da saukar jirage na Kaduna sakamakon matsalar tsaro da filin jirgin ke fama da ita.

’Yan bindiga sun sake kashe mutum 23 a Giwa

Haka kuma a makon nan dai ne ’yan bindiga suka sake kai hari karo na uku a kauyaku biyu na Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna inda suka sake kashe mutum 23 tare da raunata wasu da dama.

Wani mazaunin yakin da Aminiya ta tattauna da shi kuma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya auku ne ranar Litinin da daddare zuwa wayewar garin Talata.

Ganau din ya ce tun da misalin karfe 5:00 na yamma ne aka fara ganin maharan a kan babura sun dawo dauke da bindigu, inda suka sanar da jami’an Tsaro.

Kauyakun da ’yan bindiga suka kutsa su ne Anguwar Maiwa da Kanwa duk a cikin Karamar Hukumar.

Ganau din ya ce a sakamakon harin, ’yan bindigar sun sake kashe musu mutum 23, amma ya zuwa yanzu sun gano gawar mutum 22 saura gawar mutum daya.

Ya kuma ce maharan sun kuma raunata mutane da dama, sun kuma kona musu gidaje da Masallatai da Coci-Coci, duk a daren.

Sai dai ya ce a wannan karon, jami’an tsaro na hadin gwiwa sun kawo dauki kuma sun ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace, su kuma maharan an kashe wasu daga cikin su da dama.