✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka kai hari kauyen Duba a Katsina

Wannan dai wata masifa ce Allah ke jarabtar mu da ita.

’Yan bindiga sun kai hari kauyen Duba da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina tare da kashe mutum 12, wasu kuma da dama suka ji rauni.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce sun sami rahoton kisan  mutum 12, yayin da mutun shida suka samu raunuka.

Garin Duba na daga cikin garuruwa ko kauyukan da ’yan bindiga suka saba kai hari a lokutan baya.

To sai dai abin ya yi sauki daga baya, wanda har hakan ma ya sa sauran mutanen ’yan kauyukan da ke zagaye da garin sukan kawo dabbobin su a garin su kwana saboda irin yadda suka samu zaman lafiya a sashen.

Sai dai kamar yadda wani mai suna Amadu ya shaida wa wakilin Aminiya ya ce, “tun wajen bayan sallar la’asar muka fara samun labarin cewa ana ganin wadannan ’yan bindiga su na fitowa daga cikin daji, can wajen Singi, inda suke biyowa ta wajen garin Labo har zuwa garin Yara.

“To sai aka ce suna taruwa can wajen wani dutse da ake kira Dutse mai zane kusa da Randa a kan hanyar zuwa Jibiya daga Batsari.

“Ba mu yi tunanin za su shigo mana ba, domin inda suka tarun nan yammacin mu kadan.

“Kuma a wasu lokutan muna jin labarin suna wucewa ta wannan wuri.

“Can bayan la’asar sakaliya, sai muka rika jin harbe-harbe ta ko’ina yana tashi.

“Tun da babu shiri, sai kowa ya yi ta kan shi domin gaskiya babu wanda zai ce ga yawan ’yan bindigar.

“Kuma sun yi wa garin kawanya sai wanda Allah ya fidda kawai don haka muka samu kanmu a tsakiyarsu.

“Harbi kawai suke yi babu kakkautawa, wasu kuma na can suna kora dabbobi, wasu kuma suna shiga cikin shaguna suna kwasar kaya.

“Ni kai na in nace maka ga yadda aka yi na tsira nayi karya, Allah dai ya fitar da ni.”

Shi kuwa wani da aka tuntube yana cikin zubar da hawayen bakin ciki, ya ce, “wannan dai wata masifa ce Allah ke jarabtar mu da ita.

“’Yan uwa na biyu ga su nan kwance a gaba na ko rufe su ba a yi ba. Kawai dai mun barwa Allah lamarin shi.”

Da wakilin Aminiya ta so jin ko sun samu dauki musamman daga jami’an tsaro, sai ya ce, “Haba malam? Wane jami’an tsaro?

“Tun lokacin da aka ga mutanan nan suna tattaruwa aka shaida masu, amma babu wanda muka gani, kuma su ’yan bindigar ba wai cikin duhu ne suke tattaruwa ba, kai dai kawai kamar yadda na ce, mun bar wa Allah.”

Aminiya ta zanta da wani wanda ya bayyana kansa da sunan, daya daga cikin wadanda aka korawa dabbobi.

A cewar Malam, “Ina zaton ganin irin yadda ake kawo dabbobi daga makwabta su kwana nan ya sanya wadannan mutane suka kawo mana wannan harin.

“Kuma sun yi barna bakin iyakar son ran su kuma sun tafi babu wani abin da aka yi.

Kusan dukkan wadanda Aminiya ta zanta da su ta wayar salula, sun bayyana bacin ransu a kan irin yadda aka mayar da rayuwar su ba bakin komai ba, bayan kullum ana cewa wai ana samun tsaro.

Sai dai kuma wasun su sun yarda da cewa tabbas sai da dan gari a kan ci gari dangane da ire iren wadannan hare hare da ake kawo musu da  kuma lokutan da ake kawowa.

“Hakika, mun yarda da maganar Gwamna Masari a kan cewa kowa ya nemi makamin kare kan shi” in ji wani mazaunin kauyen.

Saurari: Abin Da Ya sa Hukumomi Suka Kasa Shawo Kan Kwalara