✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka sace manoma 22 a Abuja

Akwai wasu mutum 13 ‘yan gida daya daga cikin manoman 22 da aka sace.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa ’yan bindiga sun sace manoma 22 tare da kone motocin aikin noma a Abuja, babban birnin kasar.

Lamarin ya faru ne a kan al’ummar Rafin Daji da ke iyaka da Jihar Neja a gundumar Gurdi ta Karamar Hukumar Abaji.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, ASP Oduniyi Omotayo, ya ce an sace manoman ne suna tsaka da aiki a gonakinsu.

ASP Omotayo ya ce ana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su inda ake ci gaba da sa ido a kan al’umma.

Wani manomi da ya tsallake rijiya da baya da kyar, Sa’idu Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na ranar Alhamis, inda ‘yan bindigar da yawansu dauke da bindigogi kirar AK-47 suka far wa manoman da suke noma a yankin.

Ya ce ‘yan bindigar wadanda suka yi ta harbin iska kafin su tafi da manoman, sun kona taraktoci biyu da ake amfani da su a wata babbar gona da ke yankin.

A cewar Sa’idu, akwai wasu mutum 13 ‘yan gida daya daga cikin manoman 22 da aka sace.

Ya bayyana sunayen ’yan gida dayan 13 da aka sace da suka hada da; Ismaila Barde, Mustapha Barde, Nasiru Barde, Abdulkarim Barde, Sanusi Barde da Usman Barde.

Sauran sun hada da Nura Barde, Abdullahi Barde, Babawo Barde, Farida Ayuba, Hauwa Ayuba da Hussaini Abdullahi.

Ya ce “’yan gida dayan 13 da suka hada har da mata biyu suna aiki a gonakinsu daban-daban lokacin da ‘yan fashin suka far musu.

“Allah ne kawai ya cece ni yayin da na samu nasarar tserewa lokacin da ‘yan bindigan suka zo cikin ayari mai yawa, suna harbi sama. Wasu daga cikinsu sun kona taraktoci biyu da ake aikin gona da su,” inji shi.

Shi ma Hakimin gundumar Gurdi, Alhaji Bala Mohammed, ya tabbatar da sace manoma tare da kona taraktoci da ‘yan bindigar suka yi a lokacin da yake zantawa da wakilinmu ta wayar tarho a ranar Juma’a.

Ya ce har yanzu bai kai ga tantance adadin manoman da aka sace ba, ya kara da cewa mutanensa na cikin matsanancin yanayi.

‘Yan bindiga a Najeriya sun kashe fararen hula sama da 2,600 a shekarar 2021, wanda ya karu da sama da kashi 250 idan aka kwatanta da shekarar 2020, a cewar kungiyar agaji da ke tattara bayanai ta kasar.

Wannan adadi ya zarce adadin asarar rayukan fararen hula a hukumance, sakamakon hare-haren masu jihadi.

Galibin sace-sacen mutane ana yin su ne da sunan neman kudin fansa, inda wadanda ake kashewa a hannun masu garkuwar an riga an biya kudin fansar su, amma akwai fargabar cewa wasu daga cikin kungiyoyin masu garkuwa na da alaka da kungiyoyin mayakan jihadi.