✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka yi wa masu cin kasuwa kisan gilla a Filato

Wani shugaban matasa a yankin, Shafi'i Sambo, ya ce ’yan bindigar na shiga kasuwar suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

’Yan bindiga sun kai hari a wata kasuwa inda suka kashe akalla mutum bakwai tare da jikkata wasu da dama a Jihar Filato.

Maharan sun yi wa Kasuwar Pinau dirar mikiya ne da yamma inda suka bude wa mutane wuta a yayin da ake tsaka da cin kasuwa.

Wani shugaban matasa a yankin, Shafi’i Sambo, ya ce ’yan bindigar na shiga kasuwar suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Aminiya ta gano cewa ’yan bindiga sun far wa kasuwar da ke unguwar Pinau da ka Karamar Hukumar Wase ta Jihar ne  ranar Lahadi.

Gabanin harin, a ranar Laraba 8 ga Disamba, 2021, mazauna wasu kauyuka a karamar hukumar sun yi korafin cewa ’yan bindiga na shigar yankunansu.

Sun kuma koka cewa masu hada baki da ’yan bindigar suna kawo cikas ga kokarin jami’an tsaro na magance matsalar.

Wata majiya a kauyen ta ce a kwana 10 da suka gabata ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da yawa a yankin kuma sun karbi miliyoyin kudade a matsayin kudin fansa.

Majiyar ta ce, “Miliyoyi suke karba a matsayin kudin fansa, wani lokacin Naira miliyan biyu, har zuwa miliyan biyar. Kwana uku da suka wuce sun karbi Naira miliyan biyar kafin suka sako wani mutum da suka yi garkuwa da shi.”

Wakilinmu a Jos ya nemi kakakin ’yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, domin samun karin bayani, sai dai jami’in dan sandan bai amsa kiran wayan wakilin namu ko rubutaccen sakon da ya tura mishi ba.