✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan China ke mamaye filaye a Najeriya

Sun fake da kamfanonin gine-gine suna mamaye dazuka tare da yin fasakwauri

Kungiyar Kare Muhalli ta Najeirya (NEAN) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kare dazuka da ruwan kasar daga mamayar ’yan kasar China.

Kungiyar ta ce yin hakan da wuri ya zama wajibi domin alkintawa da kuma kare filaye da albarkatun kasa da Allah Ya huwace wa Najeriya daga ’yan China.

Shugaban NEAN na Kasa, Ben Iguabor da Sakatarenta, Silas Modaccai, suka ce: “Mun lura cewa wasu ’yan China da ke shigowa kasar da sunan ma’aikatan kamfanonin gine-gine sun bige da lalata dazukan kasar Najeriya domin cimma biyan bukatunsu na tattalin arziki.

“Abin takaicin shi ne yadda suke saukin samun masu mataimaka musu daga cikin ’yan Najeriya marasa kishi wajen hallaka dabbobi da itatuwan da ke cikin dazukan kasarmu.”

Sun koka game da yadda ’yan Chinan ke jan zarensu a wurin fataucin jakuna da cin naman jakunan a yankin Kudu maso Gabas bayan an yi safararsu musamman daga Arewa maso Yamma.

“Mun gano cewa naman jaki da kiraga da fatunsa na da matukar daraja kuma ana nemansa ido rufe a China, kuma ba ta iya wadata kanta da su, shi ya sa Chinasawan suka koma fasakwaurinsu daga kasashe irin Najeriya

“Baya ga kashewa da fasakwaurin jakunan daga Najeriya, yanzu ’yan China sun fara kai hari a kan ma’aikatan kare dabbobi da ke yaki da ayyukansa da masu taimaka musu.”