✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan Majalisa suka yi dambe kan kudurin karbar haraji a Ghana

’Yan majalisar sun ba wa hamata iska kan kudurin karbar haraji daga masu hada-hadar kudi ta wayar salula.

Rikici ya barke tsakanin ’yan Majalisa Dokokin Kasar Ghana kan kokarin gwamnati na fara karbar haraji daga masu hada-hadar kudade ta wayar salula.

’Yan majalisar daga jam’iyyar NPP mai mulki da ’yan jam’iyyar adawa ta NDC sun bai wa hammata iska ne a zauren majalisar.

Rikicin ya barke ne a lokacin da shugaban majalisar, Joe Osei-Owusu, yake kokarin kada kuri’ar amincewa da kudirin.

A lokacin ne ’yan jam’iyyar adawar suka bukace shi da ya zama dan kallo ba mai kada kuri’a kan kudurin ba.

Bayan an fara kada kuri’a, bangaren marasa rinjaye a majalisar suka nuna rashin amincewarsu kan jefa kuri’ar.

Lamarin ya jawo hayagaga da tayar da jijiyar wuya tsakanin bangarorin biyu na majalisar.

Daga bisani abin ya rikice aka aka shiga ba wa hamata iska a cikin majalisar, wanda hakan ya kawo tsaiko wajen jefa kuri’a game da kudurin.

Daga baya Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya bukaci hadin kan ’yan majalisar wajen yin aiki tare sa ajiye bambamcin ra’ayi ko na jam’iyya.