✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun hallaka dan bindiga a Katsina

’Yan bindigar sun kwashi kashinsu a hannu bayan sun yi yunkurin kai wa ’yan sanda harin kwanton bauna

’Yan sanda sun aika dan bindiga daya lahira a yayin da sauran ’yan ta’addan suka tsere da raunukan harbi a wani artabu da asubahin ranar Litinin a Jihar Katsina.

’Yan bindigar sun gamu da gamonsu ne a lokacin da suka yi yunkurin yi wa ’yan sandan kwanton bauna a Mahadar Magama-Hirji da ke Karamar Hukumar Jibiya ta jihar, inda suka rika barin wuta babu kakkautawa.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce “Ranar Litinin da misalin karkfe 4.30 na asubahi wasu ’yan bindiga suka rika harbi a iska za su kai wa ayarinmu hari a Magama-Hiriji; amma dakarunmu sun dakile su.

“Mun kashe daya daga cikinsu tare da kwace bindiga kirar AK47 guda daya da harsasai 90 da tsabar kudi da wasu abubuwa a hannunsa, sauran ’yan ta’addan da suka samu raunukar harbi kuma sun cika wandonsu da iska.

“Muna ci gaba da sharar yankin domin cafko ragowar ’yan ta’addan da suka tsare ko mu dauko gawarwakinsu, sannan muna gudanar da bincike,” in ji sanarwar da ya fitar.

Ya bayyana cewa jami’an rundunar guda biyu sun samu raunin harbi a yayin musayar wutar, amma an ba su kulawa a asibiti har an sallamo su.