✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda Taliban ke murnar ficewar dakarun Amurka daga Afghanistan

Rundunar Sojin Amurka ta kammala kwashe dakarunta kakaf daga Afghanistan.

Rundunar Sojin Amurka ta sanar da cewa ta kammala kwashe dakarunta kakaf daga Afghanistan bayan shafe shekaru 20 tana gumurzu a ’yan Taliban wadanda ta kira masu tsattsauran ra’ayin addini.

Tuni dai ’yan Taliban suka karbe ikon kasar ta Afghanistan gaba daya, bayan da jirgin da ke dauke da rukuni na karshe na dakarun Amurka ya bar kasar.

Hakan dai ya kawo karshen yakin da aka shafe shekara 20 ana fafatawa, kuma alamu na nuna cewa Amurka ta tafi ta bar kungiyar na da karfi fiye da lokacin da ta shiga kasar a 2001.

An dai ji karar harbe-harben bindigogi na murna a birnin Kabul, yayin da wani bidiyo ya nuna mayakan kungiyar suna shiga filin jirgin saman kasa da kasa na Hamid Karzai bayan jirgin karshe na dakarun Amurka ya bar kasar da tsakar daren ranar Litinin.

Ga kadan daga cikin hotunan muhimman abubuwan da suka wakana a kasar bayan ficewar Amurkan:

Wani jirgi mara matuki da ya tashi daga filin jirgin saman Kabul a ranar 31 ga watan Agustan 2021. (Hoto daga Aamir Qureshi/AFP)
Mayakan Taliban a saman wata motar yaki da ake kira Humvee suna tsaka da wani gangami domin bayyana murnarsu ta ficewar dakarun Amurka daga kasar.(Hoto daga Hashimi/AFP)
Kungiyar gwagwarmaya ta Afghanistan da dakarun soji masu tayar wa da ’yan Taliban kayar baya sun hallara a gundumar Khnj da ke lardin Panjshir a ranar 31 ga watan Agusta, 2021. Panjshir wani sanannen yanki mai matukar tsaro da kariyar gaske wanda da sojojin Soviet da na mayakan Taliban ba su samu damar shiga ba a lokacin rigingimun da aka fafata a baya. Yanki shi ne cibiyar masu adawa da ’yan Taliban wanda ke karkashin jagorancin Ahmad Massoud, dan sanannen jagoran Mujahidin Ahmed Sha Massoud. Hoto daga Ahmad Sahel Arman/AFP
Wasu mayakan Taliban da suka taru a kan titi yayin wani gangami a Kabul a ranar Talata, 31 ga Agusta, 2021 yayin da suke murna bayan da Amurka ta janye dukkan dakarunta daga cikin kasar. (Hoto daga Hoshan Hashimi/AFP)
Mayakan Taliban a cikin wata motar daukan kaya yayin gangami a Kabul a ranar Talata, 31 ga Agusta, 2021, inda suke murnar janyewar dukkan dakarun Amurka daga cikin kasar. (Hoto daga Hoshang Hashimi/AFP)
’Yan gwagwarmaya na jam’iyyar Ulama-e-Islam Nazryati suna murnar ficewar dakarun Amurka a Quetta. (Hoto daga Banaras Khan/AFP)
Ahmad Massoud, dan siyasa a Afghanistan kuma daya daga cikin jagororin kungiyar da ke adawa da Taliban ta National Resistance Front (NRF). Shi ne dan fitaccen jagoran nan na Mujahideen, Ahmed Sha Massoud. Wani hoto kenan da aka dauke shi a Paris a ranar 22 ga Maris, 2021. (Hoto daga Joel Saget/AFP)
Wasu daga cikin ’yan Afghanistan da suka samu damar tserewa daga kasar a tashar Filin Jirgin Sama na Dulles da ke Jihar Virginia ta Amurka bayan an kwashe su daga Kabul. Hoto daga Anna Moneymaker/Getty Images/AFP