✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan talla ke shiga karuwanci a Kano —Hisba

’Yan matan da ke zuwa talla Kano daga kauyuka na komawa karuwanci.

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta ce ’yan matan da ke zuwa yin talla a kwaryar birnin Kano daga kauyuka na komawa karuwanci.

Mataimakiyar Kwamadan Hukumar, Bangaren Mata, Ummukulthum Kassim, ta ce yawan fadawar ’yan matan cikin miyagun dabi’u ta sa Hukumar fara sintirin da dare a birnin Kano don yi wa tufkar hanci.

Ta ce, “Yawancin ’yan matan da ke zuwa talla daga kauyukan da sunan sana’a ma ba sa komawa gida kuma suna shiga karuwanci.

“Wasunsu cikinsu ma a dakin maza suke kwana inda ake lalata da su ana ba su kudi, duk da cewa a wajen gari suke zama.”

A cewarta ko a ranar Laraba, Rundunar ta yi sintiri da dare inda ta gargadi ’yan mata masu bara da su guji yin dare a wasu wurare don kada wasu maza su afka musu.

Tana kuma jaddada cewa nan ba da jimawa ba Rundunar za ta fara kama irin wadannan matan.

Da take jawabi a ranar Alhamis ta yi zargin cewa iyaye da dama sun taimaka wurin fadawar ’yan matan cikin harkar kasuwanci.

Ummukulthum ta ce wasu iyayen ba sa yi wa ’ya’yan nasu iyaka game da irin sana’o’in da suke tura su su yi birni.

Ta kuma ce Hukumar ta fara wayar da kan jama’a game da illolin bara a kan titunan Kano, kafin daga baya ta fara kamen su don tsaftace jihar daga munanan dabi’u.