✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan wasan Super Eagles suka yi hutu a bana

Odion Ighalo da Mikel Obi sun ziyarci Ministan Wasanni.

A daidai lokacin da ’yan wasan kwallon kafa da suke buga wasa a kasashen Turai da sauran kasashen duniya suke hutu, ’yan wasan Turai kuma suke fafatawa a gasar Euro ta bana, ’yan kwallon Najeriya sun dawo gida ne suna hutawa.

Duk da cewa wadansu daga cikin ’yan kwallon sun kare kakar ce a cikin bakin ciki, akwai wadanda suka kammala cikin murna.

Sai dai koma dai yaya ta kaya, Hausawa sun ce jiki da jini, dole yana bukatar hutu.

Wadansu daga cikin ’yan kwalloan sun tsallaka kasashen waje ne domin hutawa tare da ’yan uwansu da iyalai, wadansu kuma a nan gida suka ci gaba da hutun, inda wadansu suka yi aure, wadansu kuma suka kai ziyara ga manyan kasa, sannan wadansu suka buga wasanni a garuruwansu don nishadi.

Aminiya ta rairayo yadda wadansu daga cikin ’yan kwallon suke yin hutunsu.

Shehu Abdullahi ya angwance

Amarya Naja’atu Muhammad Suleiman da Ango Shehu Abdullahi

Dan wasan baya na Super Eagles wanda kuma ya taimaka wa Kungiyar Omnia ta kasar Kubrus (Cyprus) ta lashe gasar kasar ta bana ya yi aure ne da wata ’yar fim din Hausa, mai suna Naja’atu Muhammad Suleiman, wadda aka fi sani da Murjanatu ’Yar Baba.

An daura auren ne a Jihar Kano, inda ya biya sadakin Naira dubu 50.

Daga cikin wadanda suka halarci daurin auren akwai Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Mannir Daniya, da Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa da sauransu.

Amarya Murjanata a yanzu haka tana karatu ne a Jami’ar Northwest da ke Kano.

Shehu Abdullahi dan asalin Jihar Sakkwato ne, kuma ya buga kwallo a kungiyoyin Sokoto United da Kano Pillars a Najeriya.

A kasashen waje kuwa, ya buga kwallo a kungiyoyin Kadsia SC a Kuwait da União da Madeira a kasar Portugal da Anorthosis Famagusta a Kubrus sai Bursaspor a Turkiyya kafin ya sake komawa Kubrus a bara.

Zaidu ya ziyarci Gwamnan Kebbi

Dan wasan baya na Kungiyar FC Porto, Zaidu Sanusi ya ziyarci Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu ne, inda ya mika masa rigarsa ta kwallo.

Zaidu Sanusi da Gwamnan Jihar Kebbi

Da yake bayani a lokacin da yake tarbar dan kwallon, Gwamna Bagudu ya ce ya fara son Kungiyar FC Porto ce saboda kasancewar Zaidu dan jiharsa yana kulob din, sannan ya kara da cewa mutanen Jihar Kebbi ma suna kallo tare da son Kungiyar Porto saboda kasancewar dan uwansu Zaidu a cikinta.

Da yake godiya kan karamcin da aka yi masa, Zaidu ya yaba wa Gwamna Bagudu kan ci gaban da yake kawo wa jihar, sannan ya bukaci ya taimaka wajen kara kaimi wajen habaka harkokin wasanni a jihar.

’Yan wasa da dama sun ziyarci Gwamnan Kogi

A Jihar Kogi, ’yan wasa da dama ne suka ziyarci Gwamnan Jihar, Alhaji Yahaya Bello.

Daga cikin ’yan wasan da suka ziyarci Gwamna Yahaya Bello akwai tsohon Kyaftin din Super Eagles, Mikel Obi wanda yanzu haka yake kwallo a Kuwait.

Sai Kelechi Iheanacho na Kungiyar Leicester City ta Ingila. A ziyararsa, Mikel Obi ya shaida wa Gwamna Yahaya Bello cewa zai hada hannu da shi a duk harkokin da ya sa a gaba domin ci gaban matasa.

Peter Olayinka ma ya angwance

A Jihar Legas, dan wasan gaba na Kungiyar Slabia Prague ta kasar Czech, Peter Olayinka ya angwance da amaryarsa, Yetunde Barbabas.

Yetunde ’yar fim, ta yi fice a shirin Papa Ajasco, inda take fitowa da sunan Miss Pepeiye.

Jarumar ta taba lashe lashe Gasar Wadda Ta Fi Kyau a Abuja a shekarar 2019.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin auren akwai Odion Ighalo da a yanzu yake kwallo a kasar Saudiyya da Henry Onyekuru, da dan wasan gaba na Napoli, Bictor Osimhen, da dan wasan Kungiyar Nantes ta Faransa, Moses Simon da sauransu.

’Yan kwallo sun ziyarci gidan marayu

A wani bangaren kuma, Odion Ighalo da Samuel Chukwueze na Billareal sun ziyarci gidajen marayu ne domin tallafa musu.

Ighalo ya ziyarci gidan marayu na The Ighalo Orphanage Home, wanda nasa ne, inda ya gana da marayun sannan ya tallafa musu.

Shi kuma Chukwueze ya ziyarci wani gidan marayu ne da ke garin Umu’ahiya a Jihar Abiya, inda shi ma ya gana da marayun, sannan ya karfafa musu gwiwa tare da ba su tallafi.

’Yan wasa sun ziyarci Ministan Wasanni

Odion Ighalo da Mikel Obi sun ziyarci Ministan Wasanni, Mista Sunday Dare a ofishinsa da ke Abuja.

Jihar Kaduna

A Jihar Kaduna, dan wasan gaba na Kungiyar Almería, Sadik Umar ya buga wasannin sada zumunta ne a unguwannin Tudun Wada da cikin garin Kaduna.

Shi ma Simon Moses ya buga wasannin sada zumunta a filin wasa na Barikin Ribadu da ke Kaduna.