✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yar shekara 34 ta haifi ’ya’ya 17 a Zariya

Hawa’u Suleman mai shekaru 34 da haihuwa da ke zaune a unguwar Alfadarai cikin birnin Zariya, a jihar Kaduna ta haifi ’yan hudu a asibiti.…

Hawa’u Suleman mai shekaru 34 da haihuwa da ke zaune a unguwar Alfadarai cikin birnin Zariya, a jihar Kaduna ta haifi ’yan hudu a asibiti.

Hauwa’u ta ce ta haifi ’ya’ya 17 a haihuwa takwas da ta yi.

Ta yi wannan bayani ne a lokacin da Aminiya ta ziyarce ta a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya inda likitoci ke kula da ita da jariran nata bayan ta haihu.

Malama Hauwa’u Suleiman

Hauwa’u Suleiman, ta ce a ranar Alhamis din makon jiya ne aka kai ta Asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan inda ta saba zuwa awo.

“Bayan an kai ni sai kuma Allah Ya sa na haifi ’yan hudu lafiya lau sai dai wasu ‘yan matsaloli da ba za a rasa ba”.

Ta ce daga Asibitin Gambo Sawaba sai aka tura su zuwa Shika don ci gaba da kula da ita da jariran nata.

“Su yaran suna cikin kwalba ni kuma aka kwatar da ni a dakin masu jego ana kula da ni. An kara min jini har leda uku sannan kuma da magunguna da ake ba ni ina sha.

‘Yadda na jero ’ya’ya 17’

“Na haifi yara har 17 a haihuwa takwas da na yi. Haihuwa ta farko har zuwa ta uku da na yi duk daya daya nake haihuwa.

“Sai a haihuwa ta hudu ne da ta biyar na haifi ’yan uku-uku. Haihuwa ta shida da ta bakwai na haifi tagwaye.

‘Yan uku maza da Hauwa’u ta haifa a lokaci daya

“A wannan haihuwa ta takwas Allah Ya sa na haifi ’yan hudu – daya namiji saura ukun mata. Ka ji yadda haihuwar take.

“Idan ka hada haihuwar dukkanninsu sun zama na haifi yara 17 ke nan a cikin haihuwa takwas da na yi”, inji mai jegon.

Hauwa’u ta kara da cewa,”Kuma a gaskiya a yanzu ba ni da wata damuwa”.

Jariran na bukatar kulawa

An sanya jariran a kwalbar asibiti

Da yake bayani a game da jariran, babban likita mai kula da dakin jarirai Dakta Isa Abdulkadir ya ce yaran da aka haifa na bukatar kulawa saboda sun yi kankata kuma akwai masu ciwon shawara a cikinsu.

Sai dai ya ce suna samun sauki, babu wata damuwa sosai.

Mahaifiyarsu kuma tana kwance a dakin masu haihuwa ita ma domin samun kulawa ta musamman, inji shi.

Babban likita mai kula da dakin jarirai, Dakta Isa Abdukadir

Angon karni

Malam Suleiman Muhammad wanda shi ne uban ’ya’yan ya ce, “Na aure ta kamar shekaru 18 da suka wuce. Ita kadai ce matata, kuma ni sana’ar tukin mota nake yi.

“Duk haihuwar da matata take yi, ji nake tamkar wata kyauta ce daga Allah duk da dai ba karfi nake da shi sosai ba.

“Amma dai na zama abin sha’awa a wurin mutane, har nuna ni ake yi. Don haka ina jin dadi kwarai da gaske kuma na yi murna ina rokon Allah ya shiryar da su ya ba ni abin da zan raine su”.

Tarihin mai jego

Aminiya ta nemi jin tarihin mai jegon a wajen mahaifiyarta kamar haka:

“Sunana Saudatu Haruna, kuma ni ce mahaifiyar mai jegon. Da farko dai shi kanshi baban mai jegon mahaifiyarsa, wato kakarta, ’yan uku ne aka haife su.

“Ni kuma na taba haifar tagwaye har sau biyu. Sai kuma kanwata wadda muke uwa daya uba daya ita ma ta haifi ’yan uku.

“Don haka ka ji idan ana gado to bai wuce haka ba, sai dai kuma wannan tsari ne daga Allah”.