✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’ya’yana uku suka kone a gabana —Lebura

Ban samu damar ceto wadannan yara da ke kuka suna kiran, Baba ba.

Wani magidanci ya bayyana wa Aminiya yadda a kan idonsa wuta ta cinye ’ya’yansa uku ciki har da jariri dan mako biyu da haihuwa.

Aminiya ta bibbiyi lamarin, inda ta zanta da maigidan mai suna Mubarak Abubukar kan yadda wannan lamari ya faru:

Ko za ka bayyana mana abin da ya faru?

To ni dai ina kwance ina barci, misalin karfe 12:30 na dare, sai na ji ana tayar da ni daga barcin ana ce, “Tashi, tashi, wuta.”

Sai na tashi a firgice amma ban ga mai tayar da ni ba sai dai na ga wutar na ci a cikin dakin da muke kwance tare da matata da kuma ’ya’yana.

Wutar ta faro ne daga babban dakin kuma daga kasa wajen kujeru. Sai na yi wuf na rika tayar da matata, ina ce mata ta tashi wuta. To dama dakin a kulle yake daga can kofar babban dakin.

Mun tafi ni da ita domim bude kofar amma ta ki budewa. Lokacin da muke kiciniyar bude kofar, ashe wutar har ta zagayo.

Muka yi nasarar bude kofar muka fita sai na dawo da nufin daukar yaran tunda kofar ta bude amma abin ya gagara saboda wutar ta turnuke dakin.

Sai na zagaya ta baya wajen tagar dakin. Na fasa tagar don shiga.

To lokacin da na hau don shiga cikin dakin, dira ta a ciki ke da wuya sai na goce kafata, inda ya kasance ba na iya motsawa daga nan inda nake.

Haka Allah Ya hukunta ban samu damar ceto wadannan yara da ke kuka suna kiran, Baba ba.

Hayakin da ke cikin dakin bai ba ni damar ganin ko inda suke ba har na ji su shiru.

Hakan ya tabbatar min da cewa rai ya yi halinsa, ni kuma gani zaune.

Da ma can farko a wajen bude dakin ita na fara cewa ta je ta bude amma sai dai na gan ta a tsaye domin ta gaza budewar.

Kuma kofar ba ta taba yi mana haka ta ki budewa ba sai wannan lokaci.

 

Yaran nawa ne?

Su uku ne. Maza biyu da mace guda. Babban shi ne mai shekara biyar da rabi, sai ita mai bi masa tana da shekara uku da rabi. Sai jaririn mai mako biyu da haihuwa.

Gaskiya da Allah Ya sa na iya motsawa daga nan inda nake bayan shigowa cikin dakin, hakika da na ceto su. To amma haka Allah Ya hukunta.

 

Me kake tunani ya haddasa tashin wutar?

Gaskiya ba zan iya cewa ga abin da ya haddasa wutar ba, saboda ta fara daga kasa ne.

Amma na ji wadansu na cewa wutar lantarki ce ta haddasa ta, domin an dawo da wutar da karfe 12:00 na dare, kuma an ce an dawo da ita da karfi. Gobarar kuma ta tashi da wajen 2:30.

 

Ke nan kana da wutar lantarki a gidan?

Eh, akwai.

 

Tunda ka ce wutar ta fara daga kasa ne, ba ka tunanin ko kun bar fanka ko dutsin guga ko wani abu da ke amfani da wutar a kunne?

Babu ko daya da ke kunne. Sannan duk da akwai kayan kallo amma ba mu kunna su in za mu yi barci.

 

To ina jaririn yake a lokacin?

Yana tare da mahaifiyarsa tana ba shi nono, amma rudewa ta sa ta baro shi bisa gadon ta fita. Abu ne wanda ba mu taba gani na shiga rudu irin haka ba.

 

Ko kun samu dauki daga makwabta ko wani wuri daban?

Hakika makwabta sun taimaka bakin abin da za su iya.

Su ma hukumar kashe gobara sun zo, amma ba a kashe wutar ba har sai bayan karfe uku na dare.

Duk wani abin da ke cikin dakin babu abin da aka samu, wuta ta cinye.

Kuma wannan dakin da muke ciki ne kawai abin ya faru, amma saura dakunan biyu ba su yi ba, saboda dakuna uku ne.

Tufafin da ke jikinmu ne kawai muka tsira da su.

 

Ko kun samu tallafi daga ma’aikata?

Da farko dai ba na aikin gwamnati ko na kamfani. Lebura ne ni, wanda kullum sai na fita don in samo. Ina sana’ar gini.

Amma ba zan ce ba a samu tallafi daga jama’a bakin abin da ya sawwaka ba.

Ko masu amfani da kafar sadarwar ta zamani sun yi kuma suna iya kokarinsu na tura wa jama’a abin da ya faru, kuma bakin gwargwado ana samun dan abin da ya sawwaka.

Hatta da hukumar bayar da agajin gaggawa an tura musu abin da ya faru, ciki har da rahoton hukumar kashe gobarar.

Amma dai batun taimako kamar yadda ake tunani, har yanzu babu.

Yanzu ma wannan gidan aro ne aka ba ni in zauna tunda akwai iyaye a kusa, amma ba masu karfi ne da za su yi hidima da mu ba.

Ni kuma ga abin da Allah Ya hukunta a kaina, amma matata babu abin da ya same ta a jiki.

Sai dai ka san akwai batun rudewar rashin ’ya’ya, sai a hankali abin zai gushe amma ba a mance ba.

Ni kaina sai bayan kwana biyu da faruwar lamarin na rika ganin abin kamar a mafarki ko shirin fim.

Duk da ba mu kunna maganin sauro, amma jiya da na kunna shi saboda wata bakuwa da muke tare da ita wadda ta ce sauron na hana ta barci, sai da na farka ya fi sau biyar, kuma duk farkawar wutar nake kallo, karshe dai sai da na kashe shi sannan na samu yin barci.

Amma yanzu alhamdulillahi ana samun sauki hatta raunin da na samu.

 

Mece ce fatarka a yanzu?

To babbar fatata ba ta wuce samun taimako daga wadanda Allah Ya hore wa ba domin sake tayar da muhallin da abin da za a ci kafin warkewar wannan rauni, a kuma shiga nema kamar yadda aka saba a baya.