✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za a duba sakamakon jarabawar JAMB

Matakan da za ku bi domin samun sakamakon jarabawar cikin sauki.

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta fitar da sakamakon jarabawar (UTME) da aka zana ranar 3 ga Yuni, 2021.

An gudanar da jarabawar a dukkanin cibiyoyin da aka ware na CBT a fadin kasar nan.

 1. Yadda Pogba ya cire kwalbar giya a gabansa
 2. Mun gano Ministar da ta sayi kadarar Dala miliyan 37 a boye — EFCC

Wata sanarwa da mai magana da yawun JAMB din, Dokta Fabian Benjamin, ya fitar a ranar Laraba, ta ce sakamakon mutum 62,780 ne ya fito daga cikin dalibai 160,718 da suka zauna jarabawar.

Ga matakan da za a bi don duba sakamakon jarabawar:

 • Ziyarci shafin JAMB a https://jamb.gov.ng/efacility
 • Shiga “UTME 2021 Mock Results Notification Slip”
 • A ciki za a ga inda za a sa lambar jarabawar.
 • Idan aka sa lambar a wajen aai a danna neman sakamakon jarabawa.
 • Sai a jiya, bayan dakikoki sakamakon zai bayyana.

Kazalika, za a iya duba sakamakon jarabawar ta wannan hanya:

 1. Shiga shafin JAMB a jamb.gov.ng
 2. Saka adireshin email da lambobin sirrin da aka yi amfani da su yayin rajistar UTME 2021.
 3. Sai a danna nemo sakamako.
 4. Sakamakon jarabawar zai bayyana cikin PDF, sai a fitar da shi.