✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a duba sakamakon zaben Najeriya ta intanet

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta bude shafin intanet wanda za a rika amfani da shi wajen duba sakamakon zabe domin ingantawa tare…

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta bude shafin intanet wanda za a rika amfani da shi wajen duba sakamakon zabe domin ingantawa tare da yin komai a fili.

Kwamishinan hukumar kan yada labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ya ce INEC ta budue shafin ne don inganta yadda za a yi komai a fili tare da takaita zarge-zargen magudi a zaben Najeriya.

Hukumar ta ce tana da kwarin gwiwar cewa sabuwar fasahar za ta kara yardar da al’ummar Najeriya ke da shi a kanta.

— Yaya ake amfani da sabon shafin?

— Mai bukatar sanin sakamakon zabe sai shiga shafin https://inecelectionresults.com a intanet.

— Daga nan ya danna ‘Create new account’ wanda zai ba da damar cike bayanan mutum.

— Idan ka cike bayanan naka sai ka danna ‘Sign in’.

— Daga nan zai bude inda za ka zabi jiharka ta asali.

— Idan ka zabi jihar da ka fito sai ka danna ‘Continue’.

— Da zarar ka bi wadannan matakan shafin zai tura sako wasu lambobin zuwa email din da bayar lokacin rijistar domin a tabbatar da cewa naka ne.

— Ka bude emial dinka ka kwafo lambobin sirrin da aka tura daga emai dinka.

— Daga nan sai ka koma shafin IRev ka rubuta su akwatun da aka samar, sannan ka danna ‘Activate'”, inji Festus Okoye.

Ya ce yin hakan zai kai mutum wani shafin da zai zabi akwatu da kuma mazabar da yake son duba sakamakon zabenta.

INEC ta ce tana sa ran fara amfani da shafin sakamakon zaben daga zaben cike gurbin da za a yi a jihar Nasarawa a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, 2020