✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a fafata neman kujerar Gwamnan Jihar Yobe

Akwai batun cewa Jihar Yobe ta dade ana mata kallon jiha mai alkiblar siyasa daya.

A makon jiya ne aka bayar da izinin fara yakin neman zabe a hukumance, kamar yadda jadawalin Hukumar Zabe (INEC) ya nuna domin tunkarar zaben badi.

Sai dai Aminiya ta lura cewa tun kafin a fara harkokin kamfe din ne lamura suka fara dumama a Jihar Yobe.

Akwai ’yan takara da dama da suke son darewa karagar mulkin Jihar Yobe, wadanda za su fafata da Gwamna Mai Mala Buni, wanda shi ma yake neman komawa wa’adi na biyu.

Wannan ne ya sa Aminiya ta yi nazari tare da tankade da rairayar kowane dan takara, musamman na jam’iyyun da suka fi shahara kuma suka fi amo a siyasar ta Jihar Yobe.

Gwamna Mai Mala Buni: Jam’iyyar APC

Gwamna Mai Mala Buni shi ne Gwamnan Jihar Yobe mai ci, wanda yake karkare zangon farko na mulki a karkashin inuwar Jam’iyyar APC.

Gwamna Buni ya lashe zabensa na farko a shekarar 2019, sannan yanzu ya dawo domin neman a sake zabensa karo na biyu a zaben badi.

Shi kwararren dan siyasa ne da ya fara harkar tun daga Kansila har ya kai ga matsayin da ya kai yanzu.

Wannan kwarewa tana cikin abubuwan d ake kallo a matsayin makamin tunkarar zaben badi ga gwamnan.

Sannan wasu na cewa yana da saukin kai da rashin riko mai zafi, wanda hakan ya sa yake da saukin hada kan masu adawa.

Sannan uwa-uba akwai karfin mulki, kasancewar shi ne Gwamna mai ci, wanda hakan yana iya taimaka masa wajen lashe zabe.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin yadda yake tafiyar da mulkinsa ba tare da bude ido ba a wasu harkokin na iya zama barazana a gare shi, inda wasu suke kallon hakan a matsayin sakaci wajen gudanar da mulki.

Haka kuma akwai masu kukan cewa bai cika zama a jihar ba kamar sauran gwamnonin jihohi makwabta.

Haka kuma akwai batun cewa Jihar Yobe ta dade ana mata kallon jiha mai alkiblar siyasa daya da dadewa, wanda wasu kuma suke ganin wannan ba dalili ba ne, kasancewar ana iya canja komai musamman a siyasa ta dimokuradiyya da mutane ne ke yin zabe.

Shariff Abdullahi: Jam’iyyar PDP

Shi Alhaji Sharif Abdullahi dan takarar neman kujerar Gwamna a karkashin tutar jam’ iyyar adawa ta PDP a Jihar Yobe, inda suka fafata sau uku a zaben sharar fage tsakaninsa da Dokta Ali Tikau da kuma Alhaji Abba Gana Gwamna Mai Mala Buni, na Jam’iyyar APC, Sharif Abdullahi, na Jam’iyyar PDP Alhaji Garba Umar, na Jam’iyyar NNPP Tata yadda Allah Ya ba shi nasarar ya zama dan takarar jam’iyyar ta PDP.

Alhaji Sharif mutum ne wanda tun sake dawowa mulkin dimokuradiyya a 1999 ake damawa da shi, inda a dawowar dimokuradiyya a 1999, shi ya fara zama zababben Shugaban Karamar Hukumar Bade a wancan lokaci.

Haka nan Alhaji Sharif Abdullahi ya kuma tsaya takarar neman kujerar Majalisar Dattawa a Yobe ta Arewa a zaben 2019, shi da Sanata mai ci, Shugaban Majisar Dattawa Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, inda ya sha kashi a hannun Sanata Lawan din.

Baya ga haka kuma magoya bayan Jam’iyyar PDP na ganin cewa dan takararsu mutum ne jajirtacce da shi ma ya dade a harkokin siyasa kuma ya san ciki da wajenta kuma fitacce da ba ya bukatar talla.

Wasu kuma suna ganin kasancewarsa a PDP, wadda ita ce babbar jam’iyyar adawa zai iya taimaka masa.

Ko a jawabinsa bayan lashe zaben fid-dagwani, sai da ya ce yana da yakinin mutanen Yobe za su zabe shi domin a cewarsa, “sun gaji da mulkin gado.”

Alhaji Garba Umar: Jam’iyyar NNPP

Shi Alhaji Garba Umar kafin ya shiga harkokin siyasa, ya yi aikin gwamnati da ya kai matsayin Darakta kuma ya yi aikin banki a wasu bankuna.

Dan takarar na Jam’iyyar NNPP shi ma ya dade a harkokin siyasar Jihar Yobe, domin ya taba neman tsayawa takarar Gwamna a shekarar 2011.

Masana harkokin siyasa a jihar ta Yobe na ganin cewa babban abin da ka iya kawo masa tsaiko bai wuci jam’iyyar da ya tsaya a inuwarta ba, kasancewa jam’iyya ce da yanzu ne take kafa jijiyoyinta a kasa.

Akwai wasu ’yan takara da suke neman zama Gwamna domin jan ragamar mulkin Jihar Yobe a zaben na badi, sai dai masu sharhi a kan harkokin siyasar jihar suna ganin akalar siyasar ta fi karkata kan ’yan takara guda uku, inda mafi yawan hankalin mutane ya karkata kuma ake ganin a cikinsu za a samu Gwamna.