✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kara hasken fata cikin kankanin lokaci

A wannan karon, mun kawo muku hanyoyi da dama da za a bi a kara hasken fata.

Fatar jiki tana daya daga cikin abubuwan da suke kare jiki. Domin kafin komai ya taba cikin jiki sai ya taba fata. Don haka wajibi ne mu kula da fatar jiki.

A wannan karon, mun kawo muku hanyoyi da dama da za a bi a kara hasken fata da kula da ita a cikin kankanin lokaci.

Amfani da abubuwa kamar gurji da lemon tsami da ruwan ‘glycerin’ na cikin abubuwan da suke kare fuska daga kunar rana, sannan ya sanya ta haske da sauransu.

  • A rika shafa ruwan lemon tsami da auduga kullum da daddare kafin a kwanta barci bayan an wanke fuskar da sabulu. Yin hakan na dada wa fata haske.
  • A matse ruwan Dankalin Turawa sannan a rika shafawa a fuska a kullum kamar sau biyu; safe da yamma sai a wanke da ruwan dumi.Wannan hadi yana haskaka fata.
  • Idan biki kuma za a yi, ana son yin kwalliya ga fatar ta yi duhu, sai a samu ayaba a bare ta sannan a kwaba ayabar a shafa a fuska na tsawon minti 10 zuwa 15, sannan a wanke za a yi matukar mamakin yadda fatar za ta kara haske cikin kankanin lokaci.
  • Idan ana da fata mai yawan maiko, za a iya amfani da ruwan gurji da ruwan lemon tsami a gauraya su sannan a rika shafawa a fuska ko jiki domin samun fata mai haske.
  • A samu bawon lemo a busar da shi sai a daka a tankade, sannan a samu madara a kwaba a shafa a fuska na tsawon minti 20 shi ma sai an yi mamakin yadda fuskar take kara haske.
  • Za a iya shafa ruwan ‘glycerin’ ko ‘rose water’ a fuska domin samun fuska mai sheki da sulbi.
  • A samu ruwan kwai, sannan a yawaita shafa farin ruwan a fuska a kullum domin sanya fuska haske da sheki da kuma laushi. Idan za a iya, sai a shafa a jikin baki daya.