✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kara hasken fata cikin kankanin lokaci

Fatar jiki na daya daga cikin ababen dake kare jiki bakidaya. Domin kafin komai ya taba cikin jiki sai ya taba fata. Don haka wajibi…

Fatar jiki na daya daga cikin ababen dake kare jiki bakidaya. Domin kafin komai ya taba cikin jiki sai ya taba fata. Don haka wajibi ne mu kula da fatar jikin. A yau na kawo muku hanyoyi da dama da za’a bi domin sanin yadda za’a kara hasken fata da kuma kula ta a cikin kankanuwar lokaci. Amfani da ababe kamar su gurji da lemun tsami da ruwan ‘glycerin’ na cikin ababen dake kare fuska daga kunan rana sannan kuma ya sanyata haske da sauransu.
• A rika shafa ruwan lemun tsami da auduga kullum dare kafin a kwanta bacci bayan an wanke fuskar da sabulu. Yin hakan na dadawa fata haske.
•A matse ruwan dankalin turawa sannan a rika shafawa a fuska a kullum kamar sau biyu; safe da yamma sannan sai a wanke da ruwan dumi wannan hadin na haskaka fata.
•Idan biki kuma za a je ana son yin kwalliya ga fatar ta yi duhu, sai a samu ayaba a bare ta sannan a kwaba ayabar sai a shafa kwabin a fuska na tsawon mintuna goma zuwa sha biyar sannan a wanke za a yi matukar mamaki yadda fatar za ta kara haske cikin kankanin lokaci.
•Idan ana da fata mai yawan maiko, za a iya amfani da ruwan gurji da kuma ruwan lemun tsami a gauraya su sannan a rika shafawa a fuska ko jiki domin samun fata mai haske.
•A samu bawon lemu sannan a busar da shi sai a daka a tankade sannan a sami madara a kwaba sai a shafa a fuska na tsawon mintuna ashirin shima sai anyi mamakin yadda fuskar take kara haske.
•Za a iya shafa ruwan ‘glycerin’ ko ‘rose water’ a fuska domin samun fuska mai sheki da kuma sulbi.
• A samu ruwan kwai sannan a yawaita shafa farin ruwan a fuska a kullum domin sanya fuska haske da sheki da kuma laushi. Idan za’aiya, sai a shafa a jikin bakidaya.