✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a karkare gasar Firimiyar Ingila ta bana

A ranar 26 ga watan Yuli za a karkare gasar kwallon kafa ta Firimiyar Ingila

A ranar 26 ga watan Yuli za a karkare gasar kwallon kafa ta Firimiyar Ingila, a kakar wasa ta 2019/2020 in da za a fafata wasanni 10 tsakanin kungiyoyi 20 da ke buga gasar da misalain karfe 4 na yamma agogon Najeriya.

Zakaru a gasar:

Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ita ce ta samu nasarar lashe gasar Firimiya ta bana, bayan ta shafe shekara 30 rabonta da cin kofin.

Nasarar ta zo musu ne saura wasanni bakwai a kammala gasar, a ranar 25 ga watan Yuni, a wasan da Chelsea ta doke  Manchester City a birnin Landan.

Wasan da ya tabbatar da nasarar Liberpool a bana da tazarar maki 25 da kuma wasa 7 a hannu inda ta karya tarihin kungiyoyin Manchester City da Manchester United.

Kungiyar Manchester United da Manchester City da Arsenal suna daga cikin kungiyoyin da suka lashe gasar Firimiya kafin a karkare wasanni.

A kakar wasa ta 1999/2000 Manchester United ta lashe saura wasa 4 a kammala gasar.

Ta kuma sake lashewa 2000/2oo1 saura wasa 5.

A kakar wasa ta 2003/2004 kungiyar Asenal ta lashe gasar ana saura wasa 4 a kammala.

United ta sake lashewa a 2012/2013, sai Manchester City ta lashe a 2017/2018 saura wasa 5 a kamala gasar.

Zakarun Turai:

Kungiyoyin da suka samu nasarar shiga gasar zakarun kai tsaye Turai su ne Liverpool, wacce ita ce zakara a gasar Firimiya.

Sai kuma Manchester City wacce ta kare a mataki na biyu.

Wadannan kungiyoyi suna daga cikin kungiyoyi 4 da za su wakilci kasar Ingila a gasar zakarun Turai ta badi.

Gumurzu:

Kungiyar Chelsea da Manchester United da Liecester City suna daga cikin wadanda za su fafata a wasan karshe wanda za a buga a ranar Lahadi 26 ga watan Yuli.

Manchester United da maki 63, sai Liecester wacce da maki 62 sai kuma Chelsea da maki 63 bayan kowacce daga cikinsu ta buga wasanni 37.

Manchester tana bukatar lashe wasanta na karshe tsakaninta da Liecester ko ta yi canjaras.

Ita kuma Liecester tana bukatar dole ta ci wasanta da United idan har kowacce kungiya tana bukatar buga gasar Zakarun Turai.

Sai Chealsea wacce take da babban kalubale wanda dole sai ta doke kungiyar Wolberhamton kafin ta samu shiga wasan Zakarun Turai ta badi ko ta buga kunnen doki.

Gasar Europa League:

Kungiyar Wolberhampton ta buga wasa 37 da maki 59 sai Tottenham da ta buga wasa 37 da maki 58.

Kowacce kungiya tana da bukatar samun maki, dole kungiya daya ce za ta tsallake daga cikinsu.

Ajin ba yabo:

Kungiyoyin da suka kare a mataki na tsakiya wadanda ba za su buga wasan Zakarun Turai ba, sun hada da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da Sheffield da kuma Burnley United. 

Kokawar tsallake fadawa rukuni na biyu: 

Tsakanin Watford da Aston Villa inda kowacce kungiya ta buga wasanni 37 da maki 34.

Sai kuma kungiyar Brighton da ita ma ta yi wasa 37 ta samu maki 34.

Duk kungiyar da ta kasa samun nasarar da ta dace za ta iya fadawa ajin Championship.

Bournemouth, idan ta yi kwazo tana iya sa rai.

Dole kungiya daya daga cikinsu ta fado rukuni na biyu.

Rukunin Championship

Kungiyoyin kwallon kafa da za su fada rukunin Championship sun hada da Norwich City wacce ta yi wasa 37 ta samu maki 21.

Ita ma kungiyar Bournemouth ta yi wasa 37 da ta tashid a maki 31, amma tana iya sa rai idan ta ci wasa da kwallaye masu yawa, sannan idan wasu kungiyoyin suka yi rashin nasara.

Zura kwallaye:

Jamie Bardy na Leicester shi ne kan gaba da kwallaye 23.

Danny Ings na Southampton na bi masa da kwallo 21 sai Pierre-Emerick Aubameyang na Arsenal da kwallo 20.

Mohamed Salah na Liverpool da Raheem Sterling na Man City kowannensu na da kwallaye 19.

Marcus Rashford na Man United da Anthony Martial da Sadio Mané na Liber Poll, kowanne yana da kwallaye 17.

Saura wasa daya a karkare gasar ta bana.